Wayewar Kan Mutanen Egypt wadda a turance ake kira da “Egyptian Civilization” tana daya daga cikin farko farkon wayewar kai da mutane suka samu a tarihin duniya. Ita wannan Wayewar Kan Mutane da aka samu a Egypt ta bunkasa ne a bakin gabar Kogin da ake kira Nile a tsakanin shekaru 3100 zuwa wajejen 2686 kafin …
Wayewar Kan Mutanen India wato Indian Civilization ita ma tana cikin na farko a cikin wayewar kai da mutane suka fara samu a duniya. Ita Wayewar Kan Mutanen India ta fara ne a Kwarin Indus dake tsakanin jerin duwatsun Himalaya da na Hindu Kush a arewa, da kuma duwatsun Sulaiman daga yamma. Kuma wannan Wayewar ta …
Wayewar Kai ta Mesopotamia wadda a turance ake kira da Mesopotamian Civilization ta bunkasa ne a yankin Kwarin Mesopotamia dake tsakanin Kogunan Tigris da kuma Eupharates a yankunan kasar Iraq, Syria, da kuma Iran na yanzu. Kuma ta fara ne a wajejen shekara ta 3000 Miladiyya. Don haka ne, a bisa rubutaccen tarihi, babu wata …
Tsohuwar Daular Girkawa wadda a turance ake kira da Ancient Greece, wata wayewar kan mutane ce ta al’ummar kabilun Girkawa (Greeks) wadda ta samu gindin zama a birane da daban-daban masu zaman kan su da ake kira ‘Acropolis’ a yankin Tsibirin Kogin Agayen (Aegean Sea), tsakanin shekara ta 1200 kafin al-Masihu zuwa wajejen shekara ta …
Tsohuwar Daular Rum wadda a turance ake kira da “Ancient Rome” wani ci gaba ne da ya fara bayan wasu kauyuka na kabilun Latin da suka kafu a bakin kogin Tiber (Tiber river ) daga bisani suka hade guri guda inda suka zama birnin Rum a wajejen shekara ta 700 bayan al-Masihu. Wanda wannan ne …
Tarihin Samuwar Dan Adam a mahangar masana kimiyya wanda a turance ake kira da Human Evolution ya nuna cewa farkon tarihin kasantuwar dan adam ya kasance ne cikin lokacin da babu rubutu wato prehistory a turance. Saboda haka ilimin mu na farkon dan adam ya dogara ne da ilimin gano da nazarin abubuwan da dan …