Shigowar Turawa Nahiyar Africa wanda a turance muka kira da ‘Europeans in Africa‘ ya kasance wani yanayi wanda Turawa (Europeans) suka samu damar shigowa cikin Nahiyar Africa tare da mamaye nahiyar karkashin ikon su wato a turance colonial domination. Turawa sun fara shigowa cikin Nahiyar Africa tun a karni na sha hudu wato 14th century. …
Taron Berlin wanda a tarihance kuma a turance ake kira da ‘Berlin Conference‘ ya kasance wani taro wanda manyan kasashen Turai (European countries) suka gudanar domin tattauna yadda za su samu damar samun ikon mamaye nahiyar Africa. An gudanar da Taron Berlin a tsakanin watan Nuwamba na shekarar 1884 zuwa watan Janairun shekarar 1885. A …