Tarihin Juyin-Juya Halin kasar Faransa da a turance ake kira da ‘French Revolution’ wanda ya fara a shekarar 1789 zuwa 1799, wani chanji ne da mutane a Faransa (France) suka samar a tsarin shugabancin su da kuma na zamantakewar su, wanda ya haifar da rushe tsarin mulkin sarauta da kuma kafa gwamnatin yan kasa wato …
Farfadowar Ilmi da Ci Gaban Rayuwa a nahiyar Turai da a turance ake kira da ‘Renaissance‘ wani zamani ne da aka yi juyin juya hali a fannonin rayuwa kamar su ilmi falsafa (philosophy), siyasa, tattalin arziki, fasahar zane, rubuce-rubuce da kuma kimiyya da fasaha (science & technology ), a nahiyar Turai tsakanin karni na 14 …
Tsohuwar Daular Girkawa wadda a turance ake kira da Ancient Greece, wata wayewar kan mutane ce ta al’ummar kabilun Girkawa (Greeks) wadda ta samu gindin zama a birane da daban-daban masu zaman kan su da ake kira ‘Acropolis’ a yankin Tsibirin Kogin Agayen (Aegean Sea), tsakanin shekara ta 1200 kafin al-Masihu zuwa wajejen shekara ta …
Tsohuwar Daular Rum wadda a turance ake kira da “Ancient Rome” wani ci gaba ne da ya fara bayan wasu kauyuka na kabilun Latin da suka kafu a bakin kogin Tiber (Tiber river ) daga bisani suka hade guri guda inda suka zama birnin Rum a wajejen shekara ta 700 bayan al-Masihu. Wanda wannan ne …
GABATARWA Masarautar Kano Kafin Jihadi ya kasance zamani mai muhimmanci a a tarihin Masarautar Kano wadda ta kasance babbar Masarauta mai tarihi wadda take a Jihar Kano, a yankin arewacin Nigeria. Ita Masarautar Kano ta fara ne a cikin shekarar 999 Miladiyya, bayan da wani wanda ake kira Bagauda dan Bawo ya mamaye mazauna Kano …
Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano ya samo asali ne daga faruwar Jihadin Shehu Usman Danfodio, wanda ya tabbata a shekarar 1804. Tarihin Mulkin Fulani a Masarautar Kano ya samo asaline tun bayan Jihadin Fulani na Shehu Danfodio wanda ya kasance wani juyin juya hali da aka gudanar a fadin kasar Hausa da kuma wasu …
Sarakunan Kano sun kasance guda 57. Sarakunan Masarautar Kano sun fara tun daga Sarkin Kano Bagauda Dan Bawo a shekarar 999 AD zuwa Sarkin Kano na yanzu Muhammadu Sanusi II wanda ya fara sarauta cikin shekarar 2014 AD. Masana tarihin Kano sun raba jerin Sarakunan Kano zuwa gidajen sarauta guda 4 wato a turance dynasties. …
Tarihin Samuwar Dan Adam a mahangar masana kimiyya wanda a turance ake kira da Human Evolution ya nuna cewa farkon tarihin kasantuwar dan adam ya kasance ne cikin lokacin da babu rubutu wato prehistory a turance. Saboda haka ilimin mu na farkon dan adam ya dogara ne da ilimin gano da nazarin abubuwan da dan …