Masarautar Kano

SARAUTA DA HAKIMCI A MASARAUTAR KANO

Sarauta da Hakimci a Masarautar Kano ya kasance wani babban al’amari wanda yake da muhimmanci. Ita Masarautar (Kano Emirate) kasaitacciyar Masarauta ce wadda ta kafu tun a misalin shekarar 999 Miladiyya, wato fiye da shekara dubu. Kafin kafuwar Masarautar Kano, tuni akwai rukunin al’umma da tsarin shugabanci bisa bautar Tsafin Iskar Tsumburbura tare da mazaunan …