Juyin-Juya Halin Kasar Iran wani kokari ne da yan kasar Iran suka yi wanda ya basu nasarar hambarar da mulkin sarauta a kasar tare da kafa mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran. A karkashin Juyin-Juya Halin, al’ummar kasar su hambare mulkin Sarki Shah Muhammad Reza Pahlavi tare da nada Ayatollah Ruhollah Khomeini a matsayin jagoran kasar. …