Category: Hausa

A History and Culture Hub

TARIHIN ASALIN HAUSAWA

Tarihin Asalin Hausawa ya kasance babban al’amari wanda yake bukatar nutsuwa sosai. Hausawa sun kasance wata al’ummar bakaken fata wadda take zaune a yankin arewacin Nigeria ta yanzu da kuma kudancin kasar Niger ta yanzu. Hausawa sun kasance suna yin magana da harshen Hausa wanda yake daya daga cikin mafi yaduwar harsunan bakaken fatar Arewa.…
Read more

JUYIN-JUYA HALIN KASAR IRAN

Juyin-Juya Halin Kasar Iran wani kokari ne da yan kasar Iran suka yi wanda ya basu nasarar hambarar da mulkin sarauta a kasar tare da kafa mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran. A karkashin Juyin-Juya Halin, al’ummar kasar su hambare mulkin Sarki Shah Muhammad Reza Pahlavi tare da nada Ayatollah Ruhollah Khomeini a matsayin jagoran kasar.…
Read more

ZUWAN TURAWA KANO

Zuwan Turawa Kano ya kasance wani lokaci wanda Turawan Ingila (Britain) suka samu nasarar mamaye kasar Kano tare da kafa mulkin mallaka a shekarar 1903. Asalin Zuwan Turawa Kano Zuwa shekarar 1900 Turawan Ingila sun mamaye kusan daukacin Masarautu dake karkashin Daular Sokoto. Daga cikin manyan da suka gagara a mamaye su sun kasance Kano…
Read more

YAKIN BASASAR KANO

Yakin Basasar Kano wani yaki ne da ya faru a tarihin Kasar Kano a tsakanin yan biyu jikokin Sarkin Kano Ibrahim Dabo akan kujerar Sarautar Kano. Wadannan yan uwa sune Sarkin Kano Tukur da kuma Galadiman Kano Yusufu. Yakin Basasar Kano ya afku a cikin shekarar 1893, kuma an kare shi a farkon shekarar 1894…
Read more

JUYIN MULKI A NIGERIA

Juyin Mulki a Nigeria ya kasance wani kokari ko yunkuri da sojojin Nigeria suka dinga yi domin hambarar da mulkin farar hula. A tarihin Nigeria, sojoji sun kaddamar da yunkurin juyin mulki har kusan guda bakwai a tsawon shekaru ashirin da hudu wato daga shekarar 1966 zuwa shekarar 1990. Daga ciki guda biyu an hambarar…
Read more

SHIGOWAR TURAWA NAHIYAR AFRICA

Shigowar Turawa Nahiyar Africa wanda a turance muka kira da ‘Europeans in Africa‘ ya kasance wani yanayi wanda Turawa (Europeans) suka samu damar shigowa cikin Nahiyar Africa tare da mamaye nahiyar karkashin ikon su wato a turance colonial domination. Turawa sun fara shigowa cikin Nahiyar Africa tun a karni na sha hudu wato 14th century.…
Read more

TARON BERLIN (BERLIN CONFERENCE)

Taron Berlin wanda a tarihance kuma a turance ake kira da ‘Berlin Conference‘ ya kasance wani taro wanda manyan kasashen Turai (European countries) suka gudanar domin tattauna yadda za su samu damar samun ikon mamaye nahiyar Africa. An gudanar da Taron Berlin a tsakanin watan Nuwamba na shekarar 1884 zuwa watan Janairun shekarar 1885. A…
Read more

YAKE-YAKEN SARKIN KANO DABO

Yake-Yaken Sarkin Kano Dabo sun kasance wasu yake-yake ya kaddamar domin tabbatar mulkin sa da kuma kasaitar Kasar Kano. Sarkin Kano Dabo ko Ibrahim Dabo ya kasance Sarkin Kano wanda wasu suke ganin cewa yafi kowane Sarki tasiri a jerin Sarakunan Kano guda hamsin da bakwai. Dalilai da yawa kuwa sune suka hadu suka bawa…
Read more

SARKIN KANO IBRAHIM DABO

Sarkin Kano Ibrahim Dabo wani kasaitaccen sarki ne wanda ya mulki Kasar ko Masarautar Kano daga shekarar 1819 zuwa 1845. Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya kasance daya cikin mafi muhimmanci tare tasiri a jerin sarakunan da suka mulki Masarautar Kano. Yayin da wasu masana tarihin suke ganin cewa a tarihin Kasar Kano ko Masarautar Kano…
Read more

KABILUN FULANI A KANO

Kabilun Fulani a Kano ko Kasar Kasar Kano sun kasance wasu rukunan Fulani wanda suka hadu suka samar da gundarin Fulanin Kano. A kalla, Kabilun Fulani a Kano sun kai kusan rukuni fiye da goma. A bisa tarihi, Kabilun Fulani a Kano sun bayar da gudunmawa wajen kafa Masarautar Kano musamman a lokacin kaddamar da…
Read more