Harkokin LafiyaHausa

AMFANIN ZOGALE A JIKIN MUTUM

Amfanin Zogale @tarihispace.com.ng

AMFANIN ZOGALE A JIKIN MUTUM. LALLAI YANA MUHIMMANCI KU KARANTA AMFANIN ZOGALE A JIKIN MUTUM.

Ana Bukatar Jama’a su yada wannan Post zuwaga Sauran Al’umma domin Qaruwa da Juna.

1- Ana dafa ganyen zogale da zuma a sha kamar shayi domin maganin Olsa (ulcer).

2- Ana shafa danyen ganyen zogale akan goshi domin maganin ciwon kai.

3- Ga wanda ya yanke ko ya sare ko wani karfe ya ji masa ciwo, zai shafa danyen ganyen zogale inshaAllah jinin zai tsaya.

4- Ga mai fama da kuraje a jiki, ya hada garin zogale da man zaitun ya shafa.

5- Ana sanya garin zogale akan wani rauni ko gembo domin sauri warkewa.

6- Sanya garin zogale a cikin abinci yana
maganin hawan-jini da kuma karama mutum kuzari.

7- Ana dafa ganyen zogale tare da sa kanwa ‘yar kadan domin maganin ciwon shawara.

8- Ga mai fama da ciwon ido zai diga ruwan danyen zogale, haka ma mai fama da ciwon kunne.

9- Macen da ke shayarwa ta dafa furen zogale da zuma dan karin nono.

10- Wanda ke fama da yawan fitsari wato cutar Diyabetis ya rinka shan furen zogale da citta kamar shayi.

11- Idan aka tafasa furen zogale da albasa aka sha kamar shayi yana maganin sanyi.

12- Haka ma cin danyen zogale yana maganin tsutsar ciki ga yara.

13- Ana daka ganyen zogale da ‘ya’yan baure a sha da nono ko kunu yana maganin ciwon hanta.

14- Ga mai fama da sanyin kashi ko wani kumburi zai soya ‘ya’yan zogale a daka su sannan a hada da man kwakwa (man-ja) sai a shafa.

15- A daka zangarniyar zogale da ‘ya’yan da ke ciki tare da karanfani, citta, masoro da kuma kimba domin karin karfin da namiji da sa masa kuzari, haka kuma yana karawa mata nishadi.

16- A daka saiwar zogale da ‘ya’yan kankana a sha da nono yana maganin tsakuwar ciki (Apendis).

17- Haka kuma idan mutum yana fama da ciwon AIDS zogale kan radadinshi ta hanyar shan ruwan dafaffen zogale.

18- Haka kuma mai fama da Typhoid da malaria da kuma ciwon basir ko shawara, zai iya yawaita shan ruwan dafaffen zogalen domin samun sauki.

Allah kasa mu Dace da Abubuwan da muka Karanta Aameen ya Hayyu ya Qayyum.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button