Harkokin LafiyaHausa

ILLOLIN BILICHIN (BLEACHING) A JIKIN DAN ADAM

ILLOLIN BILICHIN (BLEACHING)@tarihispace.com.ng

ILLOLIN BILICHIN (BLEACHING) A JIKIN DAN ADAM. MUYI KOKARI MU KARANTA ILLOLIN BILICHIN (BLEACHING) A JIKIN DAN ADAM.

A da can baya bamusan wani abu wai shi Chanja Launin fata ba, amma kuma akwai mayikan Chanja Launin fatar, se dai ana sayansu ne domin Magance kurajen Fuska ko Makero ko Kyasbi, Amma Yanzu Ya wancin mutane suna amfani da wannan Mai ne wajen canza Launin fatarsu daga baka ta koma fara.

Amma Wasu suna amfani da man ne cikin rashin sani, la’alla zuwa shago kawai suka yi sayan Mayi In suka hange shi a cikin kwali me kyalli, a kwalba ko robar man ta sha ado, kawai sai su ce a ba su shi, Wasu kuwa da saninsu suke sayen man, amm basu san irin illar da za ta biyo bayan amfani da man ba, walau a kusa ko a nan gaba, saboda kawai suna so su yi gayu, su fito fes-fes (idan ‘yanmata ne). samari su Gansu, su ce ‘kai wannan yarinyar ta kara kyau, da gani ta samu hutu.

Idan kuwa samari ne suna so su birge ‘yan matansu, a rika cewa ‘kai gayen nan fa ya iya wanka, dubi yadda yake wani kyalli’ da dai sauran maganganu iri-iri, na taya bera bari!

Akwai bayanai masu gamsarwa a kan amfani da Mai domin ya saka fata fari a cikin wannan al’umman ta Hangar magungunan mu na Gargajiya, da su yakamata ku rinka yin Chanjin Launin Fata.

Tabbas an fi sanin mata da wannan Dabi’a, domin kuwa mafi yawancin mata a cikin jama’a sun fi mayar da hankali wajan canza launin jikinsu a lokacin balaga.

Duk da irin jan kunne da masana suke yi wajan anfani da wannan Mai, bai sa an dena anfani da shi ba.

Kamar yadda masana suka yi bayani, wannan man na canza kalar fata yana da illoli kamar Haka;-

1-Yanasa raunin karfin fata
2- Yana haddasa ciwon daji (cancer)
3- Mace me ciki kuma yana kawo lalacewar Dantayin cikinta
4- kawo juyayin mahaifa
5- Yana rage Kaurin Data
6- Yana sa zubar jini Sosai In mutun Yaji ciwo
7- Yana sa Mutum Yazama kamar Dodo Idan Ya daina Amfani dashi.

Dan Haka muna Baku Shawara kuyi Hakuri da amfani da Wadannan Mayikan, Ku komawa abubuwan tira fata na Asali, wato na Gargajiya saboda su suna ma Kara lafiya ne ajikin Dan Adam.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button