Harkokin LafiyaHausa

AMFANIN GANYEN/GARIN MAGARYA

Ganyen/Garin Magarya@tarihispace.com.ng

AMFANIN GANYEN/GARIN MAGARYA. YANA DA MATUKAR AMFANI KU KARANTA AMFANIN GANYEN/GARIN MAGARYA GA LAFIYAR DAN ADAM.

Itaciyar magarya wadda akafisani da (Assidir) a larabce itaciyace mai albarka da daddeden tarihi, Tunkafin zuwan musulinci ana amfani dashi kuma bayan zuwan musulinci Annabi s.a.w ya tabbatar da amfaninsa duk da su turawan yamma sai afarkon karni na shatara suka sanshi.

Magarya yana kunshe da magunguna masu matukar mahimmanci ga jikin dan Adam kuma yana da karfin kashe kwayoyin cuta cikin dan kankanin lokaci magarya Antibiotic ne mai karfin gaske kuma cikin ikon Allah bashi da wani illa wato side effects na azo agani.

KADAN DAGA CIKIN AMFANINTA

1. Ciwon daji (cancer) : Idan ana dafa garin magarya anasha da
zuma yana kashe kwayar cutar daji koda nacikin jini ne idan
kuma Yayi miki sai arinka dafa garin magaryar da ruwan khal
ana wanke wurin mikin idan an wanke sai a barbada garin magaryar.

2. Yanada karfin yaqar cutar fata kamar su tautau, makero,
Kanzuwa da sauransu sai A kwaba shi da zuma arinkasha Ana shafawa a Wurin da abin ya shafa.

3. Yana tsaftace jini domin Yana dauke da sinadarin Saponin,alkaloid da triterpenoid wadannan Sinadaraine masu tsaftace Jini.

4. Shansa da ruwan zafi yana magance gajiya da ciwon Jiki.

5. Yana magance ulcer idan ana shansa da madara ko zuma.

6. Yana taimakawa hanta ya hanashi jin ciwo da cututtuka.

7. Yana daidaita nauyin mutun.

8. Yana tsaida zawo cikin kankanin lokaci idan aka Shashi da ruwa ko koko.

9. Yana miqar da kasusuwa musamman ga mai karaya.

10. Yana maganin rashin shaawa ga mata idan suna tsarki dashi kuma Suna shansa da madara. Wallahu
Alalam.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button