HausaSoyayya

Alamomi 10 Da Zaka Gane Kawar Budurwarka Tana Sonka

Kawar Budurwarka @tarihispace.com.ng

Alamomi 10 Da Zaka Gane Kawar Budurwarka Tana Sonka. Tirkashi!!!, Alamomi 10 Da Zaka Gane Kawar Budurwarka Tana Sonka.

Samari har ma da magidanta dama basu da fahimtar cewa kawayen buduwaisu ko matansu suna sonsu har sai sun fito karara sun furta musu hakan wanda hakan yana da matukar wahala wajen akasarin ‘yan mata.

Ba wani abun mamaki bane idan kawar budurwarka ko matarka ta nuna maka soyayya a bayyane ko kuma a kaikaice. Saboda da akwai dalilai da damar gaske da yakansa irin wadannan matan suna son samarin kawayensu ko kuma mazan kawayensu.

Wasu suna yin hakan ne saboda kyau hali ko na halitta da mazan suke dashi, wasu kuwa saboda sha’awa ko kuma kwadayin abun hannun mazan. Wasu lokutan kuma kawayen ne da kansu suke taltawa kawayensu samarin nasu ko mazansu ba tare da sun sani ba ta hanyar kambama su ko fadin wasu bajintar da suka yi ko suke yi.

Duk da yake masu iya magana na cewa ‘ana barin halas don kunya’ kuma halas din bai haramta ba, to ya ragawa mai shiga rijiya ko ya bar halas ko kuma ya cire kunya yayi halas.

Ga wasu alamu nan da kowani namiji zai iya fahimtar aminiyar budurwarsa ko matarsa tana sonsa da aure, kamar haka:

1. Zata rika yawan ziyaran gidanku amma sai lokacin datasan kana gida.

2. Zata yi kokarin ganin ta shaku da wanda tasan kafi so.

3. Zata rika neman bukatu kai tsaye daga wajenka ba tare da shakar ka ba.

4. Zata rika nunawa matarka kishi a kaikaice, ko kuma ta rika kushe ta a lokaci zuwa lokaci a gabanka.

5. Baza ta rika jin kunyar yin kwalliyar a gabanka ba.

6. Zata rika kishi da duk wacce taga ta kusanceka ko da kuwa kuna da alaka na jini da ita.

7. A kullum burinta tayi duk abunda zata yi domin ta saka farin ciki akan abunda tasan kana so amma budurwatka ko matarka bata maka.

8. Zata rika yi maka kyauta a ranakunka na musamman.

9. Zata rika bibiyan lamuranka.

10. Zata rika damuwa da abunda ke damunka da farin ciki abun alherin da ya sameka.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button