HausaMasarautar Kano

Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi (1855-1882)

Kofar Gidan Rumfa da Tambarin Masarautar Kano @tarihispace.com.ng

Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi (1855-1882) shine dan Sarkin Kano Ibrahim Dabo. An rada masa sunan Abdullahi ne domin girmamawa ga Malam Abdullahi Dan Fodio kanin Shehu Usman Dan Fodio.

Tarihi ya bayyana Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi (1855-1882) a matsayin mutum dogo, mai kwarjini, himma, da kuma Jarumtaka.

Sarkin Abdullahi Maje-Karofi shine Sarkin Kano na 46 a jerin Sarakunan Masarautar Kano, Kuma na hudu a Sarakuna Fulani. An nada shi ne Sarkin Kano a shekarar 1855 bayan rasuwar yayan sa Sarkin Kano Usman Maje-Ringim. Tun hawa karagar mulki, Sarki Abdullahi Maje-Karofi ya tsayar da mulki mai karfi irin na Mahaifin sa Sarki Ibrahim Dabo.

Sarki Abdullahi idan ya hau karagar mulki zai fara Shari’a yakan daga yatsar sa sama yace, “Walkahi tallahi zan taka shi ko dan dana haifa ne, dukkan Wanda na samu ya taka Shari’a”. A lokacin sa ya zartar da hukuncin kisasi da kuma haddi wato Wanda ya Kashe a kashe shi. Kuma an yiwa barayi hukunci daidai da su inda ya rika yanke hannun barayi kamar yadda ALLAH MADAUKAKI YA Yi Umarni. Wannan dalili ne yasa duk Kanawa suka bishi har suke Yi masa kirari da “Abdullahi dagi maganin kasa mai tsauri” ko “Abdullahi Mai Kano”.

Sarki Maje-Karofi, Sarki ne wanda yake shiga kayan Sarauta yayi sunkun da shi inda zai nada katon rawani da kunnuwa biyu da amawali da hunu kamar yadda Sarki Dabo yake Yi. Yana shiga kokuwar Alkyabba ya rataya takobi da wukar Yanka wadda Shehu Danfodio ya ba su.

Ayyuka a Zamanin Sarkin Maje-Karofi

A zamanin Sarki Kano Abdullahi Maje-Karofi ne aka kafa Baitulmali inda ake ajiye kudin hukuma don ayyuka da Kuma taimakawa masu bukata daga cikin talakawan kasar Kano. Sauran ayyukan da yayi Kuma sun hada da gina Gidan Sarki na Nasarawa, Gidan Sarki na Takai, Gidan Birnin Bako domin yaki da Umbutawa, gina Masallacin Turaki Manya, da Kuma gina Soron Giwa.

Yake-Yake

Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi Bai zauna guri Daya ba. Ya tsaya sosai wajen kare Kasar Kano. Don haka ne yakan tashi daga wannan gari zuwa wancan. Ya san ko’ina a cikin kasar sa .

A zamanin Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi Kasar Kano tayi fama da tawayen wasu sassan Fulanin Kano. Akwai Yake-Yake da suka faru tsakanin Fulani da Umbutawa. Haka Kuma shima Sarki yayi yaki da Umbutawa da Kuma Sarkin Maradi Danbaskore.

Rasuwar Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi

Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi ya rasu a cikin shekarar 1882 a garin Karofi dake kasar Katsina a yayin da yake kan hanyar zuwa Sokoto domin Kai wa Sarkin Musulmi ziyara kamar yadda ya saba duk shekara. Sakamakon rasuwar sa ne a Karofi ta sa ake masa lakabi da “Maje-Karofi”.

 

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button