HausaSoyayya da Zaman Aure

Hanyoyi 15 da Zaka sa Matarka Cikin Farin Ciki

Masoya @tarihispace.com.ng

Hanyoyi 15 da Zaka sa Matarka Cikin Farin Ciki. Ku samu ku Karanta Hanyoyi 15 da Zaka sa Matarka Cikin Farin Ciki

1. Idan ka shiga gidan ka ce, ‘Assalamu Alaikum’ shaidan zai bar gidan! domin shaidan baya zama inda amincin Allah yake.

2. Ka rika yawan bata labarai. Saboda Allah SAW ya sanar da mu dan Adam yana son labari.

3. Ka zama mai yawan yabonta, musamman a wajen da ake kusheta ka nuna bacin ranka.

4. Ka zama mai yawan bata kyautuktuka, Kyauta tana kara dankon soyayya.

5. Ka share wasu daga cikin kuskurenta, Ka nuna baka ma san ta yi ba, Kuma dauka a matsayin abinda ya shude, karka ajiye shi a kwakwalwarka.

6. Ka nuna mata tausayawarka gareta a fili, musamman a lokacin da take da juna biyu ko take jinin al’ada.

7. Kada ka daukaka abokanka fiye da matarka (lokuta da dama wasu mazan suna fifita abokansu na karatu ko na sana,a sama da matansu).

8. Ka nuna mata babu wata budurwa dake gabanka sai ita, Ka nuna mata kullum a matsayin sabuwa take a gurinka.

9. Ka rika tunawa da ita a cikin addu,arka, Hakan zai kara kauna tsakaninku.

10. Kada ka nuna mata ce wa kana yi mata alfarma akan wani kautayi da kake mata, kamar siyan abinci.

Saboda daman hakkinta ne ka kawo mata, sannan kasan ce wa abincin kawai kake kawowa amma Allah shi ne mai ciyarwa.

11. Shaidan ne abokin gabarka ba matarka ba, Lokuta da dama idan mata da miji suka dan samu sabani har takai ana maida martani cikin fushi, to ka tuna ba daga ita bane shaaidan ne ke zugata saboda shi yana mutukar son a yi saki.

12. Ka dauki abinci a saka mata a baki, Annabi SAW yace, “abincin ba cikinta kadai zai shiga ba, zai huce har zuwa zuciyarta”.

13. Ka kasance mai yawan yi mata murmushi/fara’a domin Manzo SAW yace “duk wanda ya nunawa matarsa fara’arsa to dai – dai yake da yin sadaka”.

14. Ka zama mai yawan neman shawararta, (wasu suna ce wa ba a shawara da mata), To ku sani ce wa manzo SAW ya kasance yana shawara da matansa.

15. Karka 6oye mata damuwarka, farin cikinka ko bakin cikinka.

Domin ita magani ce a tattare dakai.

ALLAH bamu abokan zama nagari.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button