Hausa

Idan da Gaske Ciwon Ya Mace na Ya Mace ne, da Mata sun riƙa Aura wa maza ƙawayensu

Yan Mata @tarihispace.com.ng

Idan da Gaske Ciwon Ya Mace na Ya Mace ne, da Mata sun riƙa Aura wa maza ƙawayensu. Wannan haka yake, Idan da Gaske Ciwon Ya Mace na Ya Mace ne, da Mata sun riƙa Aura wa maza ƙawayensu

NASIHA GA MATA: Tare da Zainab Muhammad Michika.

 

• Da ace mata na imani da kaddara kamar yadda ya kamata su san cewa komai rubutacce ne awajen Allah. Su gane cewa kaddaranka ba ya wuceka ko wane iri ne, to da zafin kishin da suke da shi ya ragu sosai.

• Da masu aure suna sa kan su a takalman marasa aure ta fuskar yadda suke jin suna son suma suyi aure da an samu sassaucin kishi agun aure.

• Da ace masu aure suna daura kan su akan iyayen wanda basu da aure ta fuskar yadda suke jin tamkar su janyo ma ‘ya’yan su mazan aure da an samu sassaucin kishi agun mata.

• Da ace kowacce mace za ta san cewa arzikinta nata ne ba wanda ya isa ya kwace mata bare tayi tunanin wata zata zo ta hana mata jin dadin da take ciki to da an rage kishi.

• Da ace mata da gaske suke akan cewa ciwon ‘ya mace na ‘ya mace ce to da sun rika janyo na kusa dasu (Qawaye) suna aura ma mazan su.

• Da ace kishiya da kishiya zasu cire kyashi, hassada, su tsarkake zuciyoyin su su zauna da juna tamkar yaya da kanwa to, da an rika zama lafiya ba’a samu matsala ba acikin gidan aure.

•Da ace maza zasu rinka kyautata ma matan su ta fuskar kyautata mu’amala da girmamawa sannan kowacce cikin kishiyoyi su barta a matsayin ta kada su rinka fifiko akan wata to da an samu zaman lafiya agidajen kishiyoyi.

• Ban ce duka ba a samu ba, a’a, ana samun hakan koma fiye da hakan amma duk da haka wasu sai kaga Allah ya jarabce su dason zuciya da kuma sharrin shaidan saikaga ana nuna fifiko a bayyane.

Allah ka kara sassauta ma matan mu kishin da suke fama da shi ka kuma bama mazan mu ikon kyautata ma matan nasu.

AMEEN

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button