Hausa

Irin Namijin da Mace Ya Kamata ta Rike Hannu Biyu

Namijin da Mace Ya Kamata ta Rike@tarihispace.com.ng

Irin Namijin da Mace Ya Kamata ta Rike Hannu Biyu. Ya kamata Ku Karanta Irin Namijin da Mace Ya Kamata ta Rike Hannu Biyu.

Kina Haduwa Da Namiji Mai Irin Wadannan Halayen Rikeshi Gam Kin Samu Mijin Aure:

Kaman yadda muka kawo wasu alamu na dacen mijin aure kamin mace ta amince da mai sonta da aure, ga Karin wasu alamomin da suke tabbatar miki da kinyi dacen mijin aure:

1: Namijin daya damu da damuwarki.

2: Namijin da kullum sai ya kiraki ya tambayeki yadda kika kwana, kika wuni da kuma yi miki fatan tashi lafiya.

3: Namijin Da Yake Baki Lokaci Baya fakewa da aiki yayi masa yawa.

4: Namijin da yake sauraronki yake baki hankalinsa a duk lokacin da kike son zantawa dashi na muhimmi.

5: Namijin da baya jira har sai kin tambayeshi.

6: Namiji mai cika alkawari. Duk alkawarin da ya miki yana kokarin ya cika. Bana naki kadai ba har na wasu daban. Wannan ba mijin yadawa bane, rike shi gam.

7: Namiji mai furta miki kalaman so a fili, a baka da kuma kuna ku biyu.

8: Namiji mai kalamai masu kyau a lokacin farin ciki da kuma bacin ransa.

9: Namijin da yake da zumudin bashi dama yaga iyayenki ko magabatanki.

10: Namiji mai nuna miki farin cikinsa da kuma yi miki godiya a duk lokacinda kika yi abun ayaba miki. Da kallon kwalliyarki ya yaba. Idan kin kawo masa ruwa ko abinci ya jisu daban da wadanda ya saba.

11: Namiji mai amafni da wadannan kalmomin guda biyu, magiya idan zai saki masa wani abun. Ya kuma ce ya gode idan kika masa, (please and thank you).

12: Namijin da baya kunyar a ganki da shi.

Da fatan mata zasu kula da wadannan abubuwan ba su maida hankali akan aljihunsa ko abar hawansa ba. Muhammad umar wuyo

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button