Harkokin LafiyaHausa

Amfanin Aduwa Ga Lafiyar Dan’adam

Amfanin Aduwa

Amfanin Aduwa Ga Lafiyar Dan’adam. Ya kamata Ku Karanta Amfanin Aduwa Ga Lafiyar Dan’adam.

Ga dukkanin alamu zaman birni ya yi tasiri ko bata wannan al’umma fiye da yadda ake zato. Ko shakka babu a wannan lokaci yara da dama ba su san mece ce aduwa ba, ballantana su san cewa tana da matukar amfani wajen lafiyar dan’Adam. Baya ga shan aduwa da muke yi saboda dan zakin da take da shi, tana da kuma amfani a jikin bil Adama. Kadan daga cikin amfanin nata kamar yadda masana suka yi bincike a kai sun hada da, maganin shawara, tsutsar ciki, gyambon ciki, maganin fyarfyadiya, ciwon asma, zawayi, attini da dai sauran su.

Ana samun bishiyar aduwa a kasashen Afrika da Indiya da wasu kasashen kudancin Asiya da kuma na Larabawa. Mutanen Habasha na kiran aduwa da Kudkuda, Larabawa na kiran ta da Zachun, Indiya na kiran ta Enguwa ya yinda mutanen Swahili kuma na gabashin Afrika ke kiranta Mjunju.

¹ Man Aduwa:

Idan aka matse kwallon aduwa, ana iya samun man girki da ya kai kashi 45 cikin dari, wannan mai na kwallon aduwa na da matukar amfani idan ana dafa abinci da shi. Yana kuma taimakawa wajen magance yawan Cholesterol da ke kawo toshewar hanyoyin jini da Asma da sauran cututtukan da muka ambata a baya.

² Maganin Asma (Athma): Ana iya nika kwallon aduwa a mayar da shi gari sai a rika dibar garin kimanin cokali goma ana zubawa a ruwa kimanin cikin kofi guda ana sha da safe har na tsawon kwanaki goma.

³ Maganin Tsutsar Ciki: Haka zalika, a nan kuma busar da kwallon aduwa ake yi a daka shi har sai ya zama gari sannan a rika zubawa a kunun gero ana sha lokaci bayan lokaci. In Allah ya so ya yarda za a rabu da tsutsar cikin kowace iri ce da ke cikin hanjin mutum ko kuma yara.

⁴ Maganin Gyambo: A bangaren masu fama da gyambo kuma sai su samo ganyen aduwa dakakke ko kuma a daka shi a danyensa a rika wanke gyambon da shi, cikin dan kankanin lokaci in sha Allahu gyambon zai kame ko ya bushe ba tare da wani bata lokaci ba.

⁵ Maganin Ciwon Fatar Jiki: A nan kuma sai a samu man da aka fitar daga jikin ‘ya’yan aduwa a rika shafawa a jiki baki daya, yana maganin kurajen jiki sosai, ka zalika yana maganin sanyin kashi.

⁶ Maganin Kamuwa Da Fitsarin Jini: A kan daka bawon aduwa har sai ya zama gari, sannan a sanya a cikin ruwan da yara kan yi wanka da shi, misali kamar kududdufi domin kashe kwayoin dake haddasa fitsarin jini da sauran wasu kwayoyin cututtuka irin su kurkunu da sauran su. Sai dai kuma wannan yana iya kashe kifaye da su dodon kodi dake cikin ruwan ko kududdufin.

⁷ Maganin Kunburin Sawu Ko Na Jiki: Domin maganin wannan cuta ta kumburin sawu ko jiki, sai a dafa saiwar aduwa a cikin miya a rika sha. Ka zalika yana yin har maganin ciwon ciki.

⁸ Amfanin Bagaruwa A Jikin Dan’adam
Bagaruwa, itacenta, ganyenta da ‘ya’yanta duka maganine kuma ana samunta a kasashe da dama kamar su india, austaralia, Da kuma kasashen Larabawa sannan an fi samunta a busashshen wuri.

Bagaruwa tana saurin saukar da masassara da kuma tsayar da zubar jini ko wane iri kuma ana amfani da ita wajen yiwa dabbobi magani.

Ana amfani da bagaruwa wajen magance matsalolin fata, tsutsar ciki, tana karawa hakora karfi da haske kuma tana maganin ciwon hakora, sannan ana amfani da ita wajen magance matsalar ciwon suga, haka tana saurin saukar da gudawa.

A binciken da Dakta Bikram Chauhan ya yi a India a shekarar 1999, ya gano tana maganin hepatitis C birus.

Yanda Za A Yi Amfani Da Ita:
Konewa, Toyewa Ko Kuma Gogewa: Ana daka ‘ya’yan bagaruwa a rika zubawa ko kuma a samu ‘ya’yanta wanda ba su bushe ba a rika matsa ruwanta a cikin wurin

Ciwon Hakori, Haskensu Ko Kuma Warin Baki: Ana samun iccen bagaruwa a yi asawaki da shi kullum in za a kwanta bacci haka idan aka tashi daga bacci. Ko kuma a samu itacenta a hada ta da jar kanwa a rinka kuskure baki da shi duk idan za a kwanta da kuma idan an tashi bacci.

Lafiyar Mata: A hada ‘ya’yan bagaruwa da itacenta da rihatul-hulbi a sa a wuta idan suka tafasa sai a sauke a tace a samu buta a zuba a rika tsalki da shi bayan minti 10 sai a sake sarki wannan yana matse macce kuma yana maganin toilet Infection sannan yana saka ta kamshi sosai.

Matsalar idanu: A samu ganyen bagaruwa a tafasa, idan ya tafasu a juye a buta a rika wanke idanu da shi duk safiya wannan yana kawar da jan ido da kuma yanar ido in sha Allahu.

Amfanin ta ga Maza: Duk wanda ke saurin biyan bukata kafin matarsa zai iya amfani da ‘ya’yan bagaruwa ya daka ta sai ya zuba ruwa ya rinka sha In sha Allahu zai ga cenji.

Godiya ga Allah (SWT) da ya saukar mana da bagaruwa da sauran abubuwa na yau da kullum. Allah ya kara mana Lafiya, amin.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button