Harkokin LafiyaHausa

Matsalar Ciwon Laka da Alamomin sa

 

Matsalar Ciwon Laka @tarihispace.com.ng

Matsalar Ciwon Laka da Alamomin sa. Ya kamata Ku Karanta Matsalar Ciwon Laka da Alamomin sa.

Matsalar ciwon laka da shanyewar sassan jiki na da gagarumar illa ga gangan jiki, tunani, kwanciyar hankali, walwala, saduwa da iyali, tattalin arziƙi da sauransu.

Alamomin Ciwon Laka

Alamomin ciwon laka sun dogara ne da inda rauni ko lahani ya faru. Misali, idan raunin ya faru a wuya, to daga wuya zuwa ƙasa ne zai sami matsala, wannan ya haɗa da hannaye, gangan jiki, ƙafafu da sauransu. Haka nan, idan raunin a daidai wani ƙashi daga ƙasusuwan gadon baya ne, to daga nan har zuwa ƙasa matsalar za ta faru.

Bugu da ƙari, matsalolin ciwon laka sun sake dogara da girman raunin da lakar ta samu. Misali, a wani lokacin lakar tana tsinkewa gaba ɗaya ne. A wannan yanayi za a samu yankewar saƙonnin ƙwaƙwalwa zuwa sauran sassan jiki. A wani lokacin kuma ta sami rauni ko ciwon da zai hana ta isar da saƙonni yadda ya kamata.

Alamomin sun haɗa da:

1) Kasa iya motsa hannaye ko ƙafafuwa.

2) Ɗaukewar ji a fata, kamar taɓawa, sanyi ko zafi.

3) Kasa iya riƙe fitsari ko bahaya.

4) Matsalar saduwa da iyali.

5) Matsalar numfashi da sauransu.

Abubuwan da ke haddasa ciwon laka:

1) Haɗuran ababen hawa.

2) Faɗowa daga sama.

3) Harbin bindiga ko suka da makami.

4) Cututtuka kamar sankara/daji, tarin fuka(tarinTB), da sauransu.

FAƊAKARWA: Ga duk wanda haɗarin abin-hawa ko faɗowa daga sama ya ritsa da shi ana ƙaddara cewa ya sami rauni a lakarsa har sai likita ya tabbatar da akasin hakan. Saboda haka, akwai matuƙar buƙatar garzayawa da waɗanda irin wannan tsautsayi ya ritsa da su zuwa asibiti.

Daga ƙarshe, wasu masu wannan matsala na buƙatar yi musu tiyata/aiki a gadon baya, yayin da wasu kuma basa buƙata.

Likitocin fisiyo (physiotherapists) ne ke ƙoƙarin farfaɗo da aikin lakar ga waɗanda akai musu tiyata/aiki da waɗanda ma ba ta kai ga yi musu ba.

Tabbatar akwai likitan fisiyo a cikin likitocin da ke kula da masu ciwon laka.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button