HausaLabaran Kasa

Wani Matashi Ya Kashe Iyayen Sa a Jihar Jigawa

Wani Matashi Ya Kashe Iyayen sa@tarihispace.com.ng

Wani Matashi Ya Kashe Iyayen Sa a Jihar Jigawa. Lallai kam, Babbar Matashin Ya Kashe Iyayen Sa a Jihar Jigawa. Wani Matashi ya Bayyana yadda ya Kashe Iyayen Sa.

Na Kashe Iyayena Saboda Suna Kirana Mahaukaci Don Ina Yabon Manzon Allah ~ Mawakin Tijjaniya Azzakiru Munkaila

Matashin da ya kashe iyayensa a jihar Jigawa, Munkaila Ahmadu, ya bayyana dalilin da yasa ya hallaka iyayen da suka haifeshi da tabarya a karamar hukumar Gagarawa.

Munkaila wanda Azzakiru ne, mawakin darikar Tijjaniyya yace iyayensa na kiransa mahaukaci kuma suna kalaman nuna rashin yarda da wakokin yabon Manzon Allah (SAW) da yake yi.

Premium Times ta ruwaito cewa Munkaila ya yi bayani a faifan bidiyo cewa ko kadan ba ya nadaman abinda yayi saboda ya yanke musu hukuncin wanda ya zagi Manzon Allah ne.

A cewarsa: “Na kashesu ne saboda sun ki amincewa da gaskiya game da Manzon Allah (SAW). Na kashesu saboda hukuncin duk wanda ya zagi Manzon Allah kisa ne, kuma babu gafara ga wanda yayi haka.”

“Na Azzakirun Manzon Allah, wannan shekarar nike da niyyar fito da bidiyon wakata kuma Idan Allah ya yarda zan yi hakan.

Za’a sake ni saboda Allah na tare da mai gaskiya, shi yasa ko a jikina bana nadama.”

“Iyayena ba sa son Manzon Allah saboda ina yabonsa, sun ce ni mahaukaci ne, na roki mahaifi ne ya goya min baya, nace masa ba na neman mata, bana caca, ban shan kwaya, kuma ban sata, amma ya ki.”

“Mahaifiyata har wajen makwabta take zuwa tana fadawa mutane ni mahaukaci ne saboda na kin zuwa gona.”

Irin wannan lamarin ya Sha faruwa a garuruwa da dama inda zaka samu mutum ya Kashe Iyayen Sa. Sai dai ana ganin Hakan tana faruwa ne sakamakon gushewar hankali ga matasan.

Koma dai meye dalili, sai dai muce ALLAH YA kyauta YA kiyaye gaba.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button