Harkokin LafiyaHausa

Ku Karanta Dalilan da Suke Kawo Shanyewar Ƙafa Ga Uwa Bayan Haihuwa

Ku Karanta Dalilan da Suke Kawo Shanyewar Ƙafa Ga Uwa Bayan Haihuwa@tarihispace.com.ng

Ku Karanta Dalilan da Suke Kawo Shanyewar Ƙafa Ga Uwa Bayan Haihuwa. Ya kamata Ku Karanta Dalilan da Suke Kawo Shanyewar Ƙafa Ga Uwa Bayan Haihuwa.

Daga cikin matsalolin da iyaye mata ke fuskanta yayin naƙuda wadda ke hana su tafiya bayan haihuwa saboda raunin ƙafafu akwai matsalar nan da ake cewa “Maternal Obstetric Palsy” a turancin likita. Wannan matsala na faruwa ne yayin naƙuda a lokacin da kan jariri ya sauko zuwa ƙugun uwa. Tsawaitar naƙuda ko kuma tangarɗar naƙudar kan sa kan jariri ya danne gungun jijiyoyin laka da suka sauko zuwa ƙugu da ƙafafu da ake cewa “lumbosacral plexus” a yaren likita.

Duk da cewa wannan matsala tana iya shafar ƙafafu biyu a lokaci guda, amma ta fi shafar ƙafa ɗaya.

Iyaye mata da suke da haɗarin samun wannan matsala sun haɗa da:

1] Gajeru; saboda ƙuncin ƙugu.

2] Naƙuda / haihuwar jaririn da kansa ya wuce matsakaicin girma, wato girman kan jaririn ya fi faɗin mafitar ƙugun.

3] Nawa ko tsawaitar naƙuda fiye da yadda aka saba gani.

4] Uwayen da suka gaza haihuwa da kansu har sai da aka temaka musu da maƙatar ungozoma domin zaƙulo kan jaririn, wato “forcep delivery” a turance.

5] Juyewa ko karkacewar jariri yayin naƙuda da sauransu.

Alamun larurar sun haɗa da:

Waɗansu alamun suna bayyana tun a lokacin naƙuda, a yayin da wasu kuma kan bayyana bayan haihuwa.

1] Ciwo daga cinya zuwa tafin sawu.

2] Rashin jin daɗi a fatar ƙafar; kamar jin tafiyar kiyashi, jin dindiris, jin kamar ana tsira allura, ko kuma jin kamar jan wutar lantarki.

3] Shanyewar ko raunin kafafu da tafin sawu.

4] Ƙwacewar fitsari da/ko bahaya.

5] Matsalar saduwa da iyali, da dai sauransu.

Sai dai, sau da yawa a kan bar iyaye matan da suka haihu a kwance saboda sun kasa tashi sakamakon rashin ƙwarin ƙafafunsu ba tare da an ɗauki matakan da suka kamata ba.

A yayin da mace ta haihu, sannan aka lura ta kasa taka ƙafafunta a tuntuɓi likitan fisiyo domin ɗaukar matakan da suka kamata.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button