HausaLabaran Kasa

YANZU-YANZU: Buhari Ya Baiwa Yayan Matarsa, Mukamin Shugaban Kamfanin Buga Kudi Na Kasa

YANZU-YANZU: Buhari Ya Baiwa Yayan Matarsa, Mukamin Shugaban Kamfanin Buga Kudi Na Kasa. Babbar Magana!!!, YANZU-YANZU: Buhari Ya Baiwa Yayan Matarsa, Mukamin Shugaban Kamfanin Buga Kudi Na Kasa.

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Ahmed Halilu a matsayin Manajan-Darakta na kamfanin buga kuɗi na ƙasa, kamar yadda jaridar DAILY NIGERIAN ta jiyo.

Halilu, wanda wan uwargidan shugaban kasa, Aisha Buhari ne, ya riƙe kamfanin a matsayin rikon kwarya bayan murabus din Abbas Masanawa a ranar 16 ga watan Mayu.

DAILY NIGERIAN ta jiyo daga majiya mai ƙarfi cewa shugaban ya amince da naɗin ne bisa shawarar gwamnan babban banki na kasa, Godwin Emefiele, wanda ke rike da mukamin shugaban hukumar NSPMC.

Halilu na da kwarewa a harkar banki ta sama da shekaru 23, inda ya yi aiki da African International Bank Limited, AIB da Zenith Bank Plc.

Ya halarci kwas na Manyan Maaikata karo na 39 a 2017 na cibiyar National Institute for Policy & Strategic Studies Kuru, Jos inda ya samu lambar girma ta na National Institute, mni.

Malam Halilu ya yi digirin farko a fannin Noma B. (Agric), Masters in Business Administration da kuma Masters in International Affairs & Diplomacy duk a Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Har ila yau, mamba ne a Cibiyar Gudanarwa ta Nijeriya, NIM.

Wannan Nadi da aka yiwa Malam Halilu ya janyo cece kuce a fadin Nigeria domin mutane suna ganin Bai dace ba. Sun Kara da cewa a irin Gwamnati ta Buhari wadda take ikirarin yakar cin hanci da rashawa da Kuma Kankane abubuwa ace wai an samu haka.

Koda yake wannan bashi ne Abu na farko irin sa da ya faru a Gwamnatin Buhari ba. Domin kuwa an samu matsaloli na abin kunya da yawa wadanda suka dabaibayewa Gwamnatin. Don haka ne Yan Nigeria da dama suka dawo daga rakiyar Gwamnatin, har ma suke ikirarin yakar Gwamnatin a Zaben 2023 Mai zuwa.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button