Hausa

Yadda Bokaye Suke Amfani Da Maniyyin Mace

Bokaye

Yadda Bokaye Suke Amfani Da Maniyyin Mace. Babbar Magana!!!, Yadda Bokaye Suke Amfani Da Maniyyin Mace.

Wannan bawai sabon abu bane, bokaye da ‘yan tsubbu sun juma suna wannan aika-aika. duk macen da taje wajan su da sunan wai takai musu aiki, Indai tayi musu, sai suce wannan aikin bazai yiwu ba sai sunyi zina da ita kafin. wasu matan kuma su yadda saboda suna neman biyan bukata.

Yanzu abin da yake faruwa shi ne; Bokaye suna yaudarar mata musamman matan aure, da sunan zasu azirtasu da kudi, amma sai anyi zina dasu a kalla kuma sukai su Uku, ko wacce za ayi zina da ita sau Uku, to wannan ruwan maniyyin dashi za a hada musu maganin samun kudi, kodai mallakar wani abu.

mata da yawa sun jima a wannan harka, mafiya yawan matan masu kudi, matan aure sune manyan kwastomomin wadannan Bokaye, tana kai aiki tana son mallaki mijinta kodai wani abu mai kama da wannan. to su kuma wadannan Bokaye bayan kudi da zasu karba sai sunyi zina da mace kafin bada tabbacin wannan aiki.

Akwai Bokan da yake iya hana mace sallah tsawon lokaci, kana tare da mace a gida baka sani ba tana zuwa wajan boka ashe ya hanata sallah, kuma dab-da lokacin da zakuyi kwanciyar aure ya mata wani maganin da zata shafa a gabanta kai duk baka sani ba.

Daga cikin wasu abubuwan da suke saka su wajan mallakar miki shi ne; sukan iya saka su anfani da Jinin haila su saka maka a abinci, kodai wani abin sha. kodai Bokan ya nemi a kawo masa rigar da zubar jikinka ya taba dashi za ayi aikin, da dai sauran abubuwa da suka shafi haka.

wannan shine halin da al’ummah mu suka samu kansu a yau, kama daga ‘yan mata, matan aure zaurawa, ba zasu roki Allah ba sai su tafi wajan Boka ya hallakar dasu, sun Gwammace haka Indai bukatar su zata biya.

Babu abin da yake yiwuwa sai da Iznin Allah, shi ma kansa boka da Allah yaso kashe shi zai yi. Yar uwa da mutuncinki, da mijinki na aure, ki tafi wajan Boka, duk da haka bai isa ba, har sai kunyi zina dashi, wannan wani Irin Cin Amana ne, Idan kika mutu a wannan yana yi me zaki cewa Allah? kin bar abin kunya wa yayanki da kuma kanki.

Yanzu shi wannan Boka da kike zuwa ki bashi jikinki, kinsan adadin matan da yayi zina dasu ire-irenki, baki sani ba, ko yana dauke da wata cuta ya saka miki a banza baki tinanin wannan?

Allah ya tsare mu tare da iyalan mu Amin.
Copied

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button