Hausa

Ku Karanta Amfanin Ganyen Bishiyar Kuka a Jikin Dan Adam

Miyar Kuka @tarihispace.com.ng

Ku Karanta Amfanin Ganyen Bishiyar Kuka a Jikin Dan Adam, ya kamata Amfanin Ganyen Bishiyar Kuka a Jikin Dan Adam.

Ganyen kuka wanda a Ingilishi suke kiransa da (baobab) na dauke da sinadarai da dama wadanda ke inganta lafiyar jiki.

Ga sinadaran da ganyar bishiyar kuka na dauke da su:

– Vitamin C

– calcium

– phosphorus

– carbohydrates

– fiber

– potassium

– protein

– lipids

– magnesium

– zinc

– sodium

– iron

– lysine

– thiamine

Yana inganta lafiya ta hanyoyi da dama, haka kuma yana magance matsaloli iri-iri da ka iya samun mutum na yau da kullum. Ga kadan daga cikin

Ga kadan daga cikin amfanin da ganyen kukar ke da shi:

1- Yana magance tari da taruwar majina a kirji.

2- Yana rage yawan zufa kamar yadda su turarukan zamani ke yi.

3- Yana rage ciwon Asthma da na koda da na madaciya.

4- Yana rage gajiya da kumburi.

5- Yana rage radadin cizon kwari.

6- Yana magance tsutsar ciki.

Bayan wadannan wata bincike ta nuna ganyar kuka tana da wassu amfanin kamar haka:

– Zazzabin maleriya

– Tarin fuka TB

– Tana ingana garkuwar jiki

– Tana ƙara jini a jiki

– Tana maganin gudawa

– Tana maganin hakori

– Tana maganin ulsa

– Tana rage ƙiba

Sai dai kuma busar da ganyen kuka a rana kamar yadda muke yi na rage masa sinadarai da a kalla kaso 50 cikin dari. An fi son a busar a inuwa.

Wannan sune alfanun Ganyen Kuka a jikin dan Adam Wanda yake bayarwa. Kuma kowa yasan cewa a kasar Hausa akwai isashen ganyen ku ka Wanda Al’umma suke bukata. Sai dai muce Jama’a ya kamata a mayar da hankali domin samun ingancin jiki

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button