HausaLabaran Kasa

Anyi Kira Ga Ɗaliban Jami’o’in Nijeriya Su Kama Sana’o’i, Mata Kuma Suje Su Yi Aure

Anyi Kira ga Ɗaliban Jami’o’in Nijeriya Su Kama Sana’o’i, Mata Suje Su Yi Aure, Domin Babu Ranar Da Za Su Kammala Karatun Su A Nijeriya. Babbar Magana!!!, Anyi Kira ga Ɗaliban Jami’o’in Nijeriya Su Kama Sana’o’i, Mata Suje Su Yi Aure, Domin Babu Ranar Da Za Su Kammala Karatun Su A Nijeriya.

…Shugaban ƙungiyar marubutan Arewacin Nijeriya na ƙasa Comr Abba Sani Pantami ya shawarci daliban Nijeriya.

Idan ba ku manta ba, tun a ranar Litinin 14 ga watan Fabarairu ne ƙungiyar malaman jami’o’i ta Najeriya, ASUU, ta tsunduma yajin aikin gargadi ga gwamnatin Najeriya na tsawon wata guda.

A yau Litinin ƙungiyar ta sanar da cigaba da yajin aikin bayan shafe sama da wata shida tana gudanar da yajin aikin gargadi.

A cikin ‘yan shekarun nan da wahala a samu wani ɗalibi da zai iya cewa ya kammala karatun zango biyu a makaranta hankali kwance, ba tare da barazanar ASUU sun shiga yajin aiki ba, wanda hakan ya sa dalibai da dama sunyi shekaru masu yawa da suka zarce a dadin shekarun da ya kamata su kammala karatun su.

Duk ɗalibin da ke son ya yi karatu babu tasgaro sai dai ya bar ƙasar ya fita ƙasar waje, ko kuma ya shiga jami’o’i masu zaman kansu, wanda hakan abune mai wuya ga ‘ya’yan talakawa duba da wasu makarantun gwamnatin ma, iyayensu ba iya ɗaukan nauyin karatun suke yi ba.

‘Yayan manyan ƙasar da na attajiran ƙasar basu ma san menene ASUU ba, a gidajen watsa labarai kawai suke jin labarin su.

A halin da muke ciki yanzu, idan muka yi duba da yadda ake ta taɓurza, da murza gashin baki tsakanin ASUU da gwamnatin Nijeriya, ba muda tabbacin yaushe za’a kawo karshen wannan yajin aikin.

Da wannan dalilan nike bawa ‘yan uwana ɗalibai shawara da su cigaba da rike sana’o’in da suka iya hannu bibbiyu, marassa sana’a suje su nemi sana’a domin su dogara da hakan. Dalibai mata idan sun samu mazajen Aure suje su yi Aure.

Ina ganin wannan shine mafi Alkhairi a garemu, don kada matasa su shagalta da aikata abubuwan da ba su dace ba, duba da yadda babban zaɓen shekarar 2023 dake karatowa, kuma zaman matasan a gida babbar baraza nace a gare mu.

Source: Rubutawa
Comr Abba Sani Pantami,
Ɗan uwanku, ɗalibi, kuma shugaban ƙungiyar marubutan Arewacin Nijeriya na ƙasa “Arewa Media Writers”.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button