Harkokin LafiyaHausa

Illolin Cire Yar-wuya Ga Lafiyar Jarirai

Illolin Cire Yar-wuya

Ku karanta Illolin cire ‘yar-wuya ga lafiyar jarirai., Ya kamata Ku karanta Illolin cire ‘yar-wuya ga lafiyar jarirai.

Al’adar cire ‘yar-wuya ga jarirai wato “traditional uvulectomy” a turancin likita, daɗaɗɗiyar al’ada ce a ƙasar Hausa. Masana kiwon lafiya sun tabbatar da cewa abin da Bahaushe ke cewa ‘yar-uwa, wacce ke da sifar tsiro ko kuma kan yatsa, a can cikin baki daga sama, wani rumbu ne da ke ɗauke da ƙwayoyin garkuwar jiki domin yaƙar cutuka daban-daban. Sai dai, al’adar Bahaushe ta gudana kan cire ‘yar wuyan ga jarirai tsawon zamani, musamman a ƙasashen Hausa da kuma wasu ƙasashen Afrika.

Malam Bahaushe dai yana ganin cewa ‘yar-wuyan wani tsiro ne da zai iya cutar da jariri yayin shayarwa ko kuma ya kawo ciwon maƙogaro can gaba. Sai dai, wannan al’ada ta yi baram-baram da binciken kiwon lafiya a yau, a maimakon haka ma, cire ‘yar-wuyan na iya jefa lafiyar jariri cikin haɗura kamar haka:

1. Yi wa jariri mummunan miki/rauni a ganɗa.

2. Ciwo tare da kumburi a ganɗa.

3. Ɓallewar jini, musamman ga jariran da kan zo da larurar tsinkewar jini bayan miki.

4. Shigar ƙwayoyin cutuka ta hanyar wuƙa ko askar da aka yi amfani da ita wajen cire ‘yar-wuyan, ko kuma shigar ƙwayoyin cutuka cikin raunin da aka yi bayan cire ‘yar-wuyan.

5. Shigar ƙwayar cuta mai janyo ƙaƙƙamewa ko kakkafewar jiki, wato “tetanus” a turance, saboda haɗarin shigar cutar ta hanyar amfani da aska mai tsatsa.

6. Matsalar shayarwa — saboda raunata hanƙa, jariri kan fuskanci wahalar haɗiyar nono yayin shayarwa.

Daga ƙarshe, likitoci sun tabbatar da cewa barin ‘yar-wuya ba shi da wata matsala ga lafiyar jariri, kuma shi ne ma mafi alfanu ga lafiyar jaririn. Kuma cire ta na iya jefa lafiyar jariri cikin haɗuran da aka ambata a sama. Don haka a kiyaye!!!

Physio Hausa/Facebook

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button