HausaLabaran Kasa

Kotu Ta Aike Da Ɗan Daudun nan Yar Dubu zuwa Gidan Yari Bayan Ya Amsa Laifinsa

Kotu Ta Aike Da Ɗan Daudun nan Yar Dubu zuwa Gidan Yari@tarihispace.com.ng

Kotu Ta Aike Da Ɗan Daudun nan Yar Dubu zuwa Gidan Yari Bayan Ya Amsa Laifinsa. Hakan yayi daidai, Kotu Ta Aike Da Ɗan Daudun nan Yar Dubu zuwa Gidan Yari Bayan Ya Amsa Laifinsa.

Kotun shari’ar Addinin Musulunci dake zamanta a Gama PRP a karamar hukumar Nasarawa ta Jahar Kano, karkashin jagorancin mai Shari’a Mallam Nura Yusif Ahmed ,kotun ta aike da dan Daudun matsahin nan mai suna Abdullahi Umar wanda ake kira da Yar Dubu zuwa gidan ajiya da gyaran hali da tarbiya.
Matashin ana zarginsa ne da zuwa kabarin wata mata ya yi bidiyo tare da cin zarafin mamaciyar.

Ana dai tuhumar Abdullahi Umar Yar Dubu da kuma wani mai suna Mumini wanda ya cika wandonsa da iska,akan laifin hada kai wajen aikata laifi da shiga makabarta domin aikta laifin dama Aikata laifin ta hanyar amfani da waya da yunkurin tayar da tarzoma da kuma laifin tunzura al’umma wanda ya sabawa sashi na 120,212,341,255,da kuma sashi na 414 na kundin penal code.

tunda fari dai ana tuhumar Abdullahi yar Dubu da laifin zuwa makabartar Medile a karamar hukumar Kumbotso Kano,inda aka binne mahaifiyar abokin fadansa mai suna mai Abun Duniya wanda shi kuma Mumumi daya cika wandonsa da iska ya yi masa bidiyo a makabartar Lokacin da yake yin fitsari akan kabarin ya na cin mutuncin mamaciyar dake kwance a kabarin sannan suka yada bidiyon a shafukan sada zumunta.

Mai gabatar da kara Aliyul Abideen yakaranta mai laifi na farko kunshin tuhumar inda nan ta ke ya amsa laifinsa sai dai ya bayyanawa kotun cewa akwai dalilinsa nayin hakan.
Mai gabatar da karar ya yi roko karkashin sashi na 276 A cikin baka na ACGl da akafa masa shaidun jin ikirari sakamakon amsa laifinsa nan ta ke .

Matashin Abdullahi Umar mazaunin kasar Nijar ne da yake zaune yanzu haka a unguwar Kurna ta jahar kano ya bayyana danasanin aikata hakan ,da cewar ‘’ina so na aure na fita daga sabgagar mutanen da ba su fita daga sabgata ba har suka ingizani na aikata wannan abu, sai yanzu na ke dasanin aikata hakan, raina ne ya baci bayan yaje har gida ya fito da mahaifiya ta waje ya ci mutuncinta sannan ya yi bidiyo ya yada a shafukan sada zumunta shi yasa nima na aikata hakan kuma yanzu na yi da sani .

Mai shari’a Mallam Nura Yusuf Ahmad ya aike da matashin zuwa gidan ajiya da gyaran hali har zuwa ranar 16 ga watan satumbar shekarar 2022 domin ci gaba da sauraran karar.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button