HausaLabaran kannywood

Wani Lauya Zai Maka Hukumar Hisbah Kotu Idan bata Dakatar da Ado Gwanja Akan Kar Ya Saki Wakar Asosa

Wani Lauya Zai Maka Hukumar Hisbah Kotu Idan bata Dakatar da Ado Gwanja Akan Kar Ya Saki Wakar Asosa. Haka yake, Wani Lauya Zai Maka Hukumar Hisbah a Kotu Idan bata Dakatar da Ado Gwanja Akan Kar Ya Saki Wakar Asosa.

Lauyan Zai Kai Hisbah Kotu A Kan Waƙar Gwanja Mai Taken ‘Asosa’

Wani lauya a jihar Kano mai suna Barista Badamasi Sulaiman Gandu,  ya yi barazanar maka Hukumar Hisbah ta jihar Kano a gaban kotu, matukar ta gaza dakatar da shahararren mawakin nan,  Ado Isa Gwanja, daga fitar da wata sabuwar waka da ya yi mai taken “Asosa”

A makon nan ne dai Gwanja ya saki somin-taɓin waƙar a kafafen sada zumunta, inda a ka gano shi yana bin wakar tare da sosa jikinsa cewa kaikayi ya kama sh

Da ya ke zantawa da manema labarai a  yau Laraba,  Barista Gandu ya ce tuni ya aike da takardun gargaɗi na kwanaki uku ga hukumomin Hisbah da Hukumar Shari’a ta jihar Kano domin su gaggauta dakatar da mawakin daga fitar da sabuwar waka

Barr. Gandu, wanda ya zargi mawakin da yin amfani da kalaman da basu daceba acikin waƙoƙinsa, ya nuna cewa barin irin waɗannan wakokin a cikin al’umma zai kawo cikas wajen tarbiyyar yara masu tasowa.

Lauyan ya ce,  kamata ya yi gwamnatin jihar Kano ta ɗauki mawakin aiki a karkashin hukumar Hisbah domin yin amfani da hikimarsa wajen faɗakar da al’umma saɓanin yadda ya ke amfani da hikimar ta wata hanya daba

A ƙarshe, lauyan ya jaddada barazanar maka hukumar Hisbah agaban kotu matukar ta haura kwana uku bata dakatar da mawakin daga fitar da sabuwar waƙar.

Wasu Kuma mutane sun bukaci da ita ma Hukumar Tace Fina-finai ta Jihar Kano akan ta Hana Gwanjan sakin wakar. Domin sun sakin wakar zai Iya janyo lalata tarbiyyar matasa a Jihar Kano Baki daya.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button