HausaLabaran Duniya

Kalli Yadda Kyawawan Yan Mata Ke Nuna Kwalliya a Bikin Ashenda a Kasar Habasha

Kabilar kasar Habasha

Kalli Yadda Kyawawan Yan Mata Ke Nuna Kwalliya a Bikin Ashenda a Kasar Habasha. Wannan haka yake, Kalli Yadda Kyawawan Yan Mata Ke Nuna Kwalliya a Bikin Ashenda a Kasar Habasha.

Yadda Kyawawan Ƴan Mata Sukan Bayyana A Wajen Bikin Ashenda Na Ƙabilar Tigarawa Dake Ƙasar Habasha wato Ethiopia.

Bikin Ashada da Tigarawa ke gudanarwa duk Shekara daga ranar 16 ga watan Agusta har zuwa ranar 26 na kowane watan Agustan Shekara a yankin Tigray dake Ƙasar Habasha(Ethiopia) ,a tsakannin ƙabilu Tigarawa da Eritawa.

Ashenda! Bikine na Mata Zallah da ake yi a kowace Shekara a watan Agusta a garin Tigray na ƙasar Habasha, don tabbatar da farin ciki ga Mata, ya kan zo da abubuwa na kawata Jiki, Kwalliya, kaɗe-kaɗe da raye-raye, tare da rawa don girmama Darajar Mace, inda yan matan da suka halarci bikin sukan Samu kyaututtukan da suka haɗa da Abinci, da abun Sha, tare da kuɗaɗe daga Al’ummar baki ɗaya.

Bikin Ashenda

Ko da yake a wajen Tigarawa, bikin yana da Asali a addini ake tunawa da shi tun da jimawa iyaye da kakanni, domin girmamawa ga Maryama, Mahaifiyar Annabi Isah A.S, da wani Namiji bai taba Hawanta ba(Kusantarta), inda tun daga lokacin aka mayar da Bikin wani fili na girmama Y’anci ga jinsin Mata,tare da kin amincewa da cin Zarafi da take Hakkin mata.

Bikin na Ashenda, wanda aka fi Sani da “RANAR MATA” ya kasance abun Jira da marmari ga yan Matan Tigarawa, wadanda suka kai munzalin Shekarun Balaga, sukanyi Shiri na musamman don Jira da tarbar bikin “Ashenda” a manyan Watanni.

Kafin zuwan ranar bikin, gungun ƴan matan, sukanyi Shirin Hutu, tare da siyan Sababbin Sutturu, ziyartar guraren gyaran Gashi,Shirya Ganguna(Domin cashewa), tare da Samo Ciyayin da suke kira da Ciyayen “ASHENDA”, wanda zasu Daura a kirjiinsu a madadin Suttura a ranar Bikin.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button