HausaLabaran Kasa

Abin Sha’awa, Kalli Yadda Wani Matashi dan Jihar Kebbi Ya Kera Mota

Matashi dan Jihar Kebbi

Abin Sha’awa, Kalli Yadda Wani Matashi dan Jihar Kebbi Ya Kera Mota. Tirkashi, Kuma Abin Sha’awa, Kalli Yadda Wani Matashi dan Jihar Kebbi Ya Kera Mota.

Wani Matashi Mai suna Muzammil Umar daga Jihar Kebbi Wanda ya kasance fasihi ya kirkiro wata babbar mota Mai ban sha’awa. Motar wadda take daga cikin ta kamar daki tayi kyau matuka da gaske.

A wannan makon ne Matashin ya kammala kera motar wadda aka yi yaron nuna ta ga Al’ummar Jihar. Mutane masu yawan gaske ne suka taru domin su shaida da idon su. Kuma sun nuna farin ciki da annashuwa.

Jama’ar da suka taru a gurin sun bayyana matashin a matsayin fasihi Kuma Jarumi. Sun Kara da kira ga Gwamnatin Nigeria da ta Jihar Kebbi akan su taimaki matashin domin a amfana da basirar da ALLAH YA azurta shi da ita.

Idan Mai karatu yayi la’akari zai fahimci cewa a Nigeria akwai fasihan matasa Wanda suke da kwazo wajen yin kere-keren zamani da suka shafi mota, jirgi, Babur, da injina.

Amma abin takaici a Nigeria irin wadannan matasan ana barin ba tare da tallafa musu ba. Har ta Kai ana yin asarar fasahar su. Don haka ne wannan shafin mu ma muke kira ga Gwamnatin Nigeria da ta Jihar Kebbi akan su tallafawa wannan matashin.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button