HausaLabaran kannywood

Abin da Sheikh Goni Aisami Ya Fada Min Kafin Na Harbe Shi

 

Wanda ya Kashe Sheikh Goni Aisami @tarihispace.com.ngAbin da Sheikh Goni Aisami Ya Fada Min Kafin Na Harbe Shi. Abin Tausayi!!!, Abin da Sheikh Goni Aisami Ya Fada Min Kafin Na Harbe Shi.

Sojan bayyana cewa Sheikh Aisami Ya Faɗi Min Da Na Ɗaga Bindiga Zan Harbe Shi, Sojan Da Ya Káshe Sheikh Aisami Ya Bayyana.

Sojan da ya káshe babban Malami a jihar Yobe Kofur John Gabriel, ya bayyana abinda Sheikh Goni Aisami ya faɗa masa yayin da ya ɗaga bindiga zai harbe shi.

Kofur John Gabriel ya ce;

“Lokacin muka kusa da Jaji-Maji kuma kofofin motar na sauke, sai na yaudare shi cewa ina jin ƙara ƙarƙashin motarsa, sai yace shima yana ganin akwai wani abu.”

“Sai ya faka motar. Yayin da ya tsaya a gefen hanya ya fita daga motar, sai na bi shi, bayan ya gama dubawa bai ga komai ba.”

“Ni kuma tuni na fito da bíndiga da harsashi lokacin da yake duba motar. Da bai ga komai ba, sai na nuna masa bíndiga, sai ya tambayeni, ‘Me na maka?” Ni kuma na bashi amsa, babu abinda kayi min.”

“Sai ya sake tambaya ta, ‘Kana son ka káshe ni ne?’ Sai na nace masa bana son káshe ka’ Sai yayi shiru. Sai na harba bíndiga don tsoratar da shi ina tunanin zai gudu. Amma bai gudu ba, sai ya shiga cikin motar, sai na bíndige shi.” Inji Kofur John.

Mutane da dama sun bayyana ra’ayin su akan cewa lallai wajibi ne a hukunta wannan sojan da kashe Sheikh Goni. Domin. Sun bayyana Sojan a matsayin Maci Amana Wanda bashi da tausayi. Wasu Kuma sun bayyana shi a matsayin babban mayaudari Wanda baza’a taba yafewa.

Source:attasfiyah24/Facebook

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button