HausaLabaran Kasa

Garin Masoyi Baya Nisa!!! Wani Matashi dan Garin Zaria Yayi Tattaki Zuwa Sokoto Wajen Yarinyar nan da aka Yankewa Kafa

Wani Matashi

Garin Masoyi Baya Nisa!!! Wani Matashi dan Garin Zaria Yayi Tattaki Zuwa Sokoto Wajen Yarinyar nan da aka Yankewa Kafa. Lallai kam, Garin Masoyi Baya Nisa!!! Wani dan Garin Zaria Yayi Tattaki Zuwa Sokoto Wajen Yarinyar nan da aka Yankewa Kafa.

Wani Matashi dan Asalin garin Zaria mai suna Ismail Basawa ya niki gari tare da tattaki har zuwa gidan su wata yarinya mai suna Fatima yar asalin garin Sokoto wadda ibtila’in yanke kafa ya fadawa sakamakon kade ta da wani matashi yayi da mota. Shi dai Ismail Basawa ya je gurin Fatima ne domin ya bayyana Mata kaunar da yake Yi mata tare da neman auren ta.

Idan mai karatu Bai manta ba, ita dai Fatima ta hadu da ibtila’in hadari ne lokacin da wani Yaro sangartacce ya buge ta da mota a yayin murnar gama karatun Sakandare a garin Sokoto. Wannan dalili ne yasa aka yanke mata kafa.

Matasa masu yawa daga garuruwa daban daban sun bayyana soyayyar su ga Fatima tare da tabbatar da cewa za su aure ta matukar ta yarda.

 

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button