HausaLabaran Duniya

Karanta Dalilin da Yasa Kasar India Tafi Yawan Mabarata a Duniya

Beggers in India @tarihispace.com.ng

Karanta Dalilin da Yasa Kasar India Tafi Yawan Mabarata a Duniya. Ya kamata Karanta Dalilin da Yasa Kasar Tafi Yawan Mabarata a Duniya.

Kasar India Kasa ce Mai girman gaske wadda ta kasance kasa ta biyu mafi yawan Jama’a a fadin duniya bayan kasar China. Domin kuwa a kasar akwai mutane akalla fiye da biliyan Daya da suke rayuwa a kasar. India tana yankin Kudancin Asia.

Kasar India ta kasance kasa Mai dinbin arziki da Kuma ci gaba musamman a harkar kiwon Lafiya da Kuma fasahar kere-keren zamani. Wannan ne yasa kasar ta zama kasa ta shida mafi karfin tattalin arziki a duniya.

Sai abin takaici, a duk fadin duniya babu kasar da tafi India yawan mabarata Wanda suke yawon bara a lungu da Sako na kasar. A cikin kasar zaka iya ganin masu bara Maza, mata, da Kuma Yara kananan Wanda adadin su yakai Miliyan goma sha hudu.

Mabarata a India

Akwai dalilai masu yawa wanda suka sa Kasar  take da yawan Mabarata. Na farko dai Al’ada tana taka rawar gani domin mafi yawancin masu yin barar sun dauki bara a matsayin gado. Wasu mabarata Kuma sun alakanta yin barar su da Addini domin suna ganin Addini ya koyar da cewa a taimaki talaka.

masu yin bara a India @tarihispace.com.ng

Don haka ne yanzu idan kaje kasar ta India zaka ga mabarata sun Taho kan ka suna rokon ka. Sai dai abin mamaki idan ka Basu kudi kadan basa karba. Misali, mafi yawancin mabaratan basa karbar sadaka da tayi kasa da Rupee Goma.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button