HausaLabaran Kasa

Manyan Birane Guda 5 Da Suka Fi Kyau a Nigeria

Manyan Birane Guda 5 Da Suka Fi Kyau a Nigeria. Wadannan sune Manyan Birane Guda 5 Da Suka Fi Kyau a Nigeria.

A Kasar Nigeria akwai birane masu yawan gaske Wanda akalla akwai mutane sama da Dubu 50 da suke rayuwa a biranen. Sai dai Kuma akwai guda Biyar Wanda suke da kyau Kuma tsarin su Yana tafiya da zamani. Wadannan biranen sun hada da Abuja, Lagos, Benin City, Calabar, da Kuma Kano.

ABUJA

Abuja @tarihispace.com.ng

Abuja shine babban birnin Kasar Nigeria wanda aka samar da shi tun a shekarar 1976. Tsohon Shugaban Nigeria na Mulkin Soja Marigayi General Murtala Muhammad ne ya tsara birnin domin ya maye gurbin Lagos a  matsayin sabuwar Hedikwatar Mulkin Nigeria. Tun 1976 ake gina Abuja har zuwa shekarar 1991 lokacin da Tsohon Shugaban Nigeria na Mulkin Soja General Ibrahim Babangida ya dawo gaba ki daya.

Birnin Abuja ya kasance birini Wanda aka tsara shi domin gudanar da Mulki, Kuma ya kasance daya daga cikin birane mafi kyau a Nahiyar Africa. Tsarin birnin Abuja ya kasance irin na babban birnin Kasar Brazil wato Brasilia.

 

LAGOS

Lagos @tarihispace.com.ng

Lagos ya kasance birni mafi girma da Kuma yawan Jama’a a Nigeria. Domin kuwa akwai mutane akalla Miliyan 15 da suke rayuwa a birnin.

Birnin Lagos ya kasance cibiyar Mulkin Nigeria tun shekarar 1960 har zuwa shekarar 1991 lokacin da aka mayar da cibiyar zuwa Abuja. Haka Kuma Lagos ta kasance babban birnin Wanda ya kasance cibiyar Kasuwancin Nigeria da ma Yammacin Nigeria Baki daya.

 

BENIN CITY

Benin City @tarihispace.com.ng

Birnin Benin shine birnin na uku mafi kyau a kasar Nigeria. A yanzu birnin shine babban birnin Jihar Edo. Sai dai birnin ya kasance tsohon birnin Wanda ya Kai kusan shekaru Dari 500 da kafuwa.

Benin City ya kasance birni mafi girma na hudu a Nigeria bayan Lagos, Kano, da Ibadan. Kuma akwai akalla mutane sama da Miliyan Daya da suke rayuwa a birnin.

 

CALABAR

Calabar @tarihispace.com.ng

Birnin Calabar birni ne mai kyau da tsari Wanda tun zamanin Turawa ake masa taken “birnin Turawa”. Domin kuwa Calabar gari ne wanda yake a bakin Tekun Atalantika  Turawa sun zauna sosai saboda yanayi Mai kyau da birnin yake da shi. Don haka ne birnin Calabar yake da tsarin irin birnin Turawa.

Birnin Calabar shine babban birnin Jihar Cross River Kuma akwai mutane akalla Dubu 500 da suke rayuwa a birnin.

 

KANO

Kano @tarihispace.com.ng

 

Kano Kasaitaccen birni ne wanda yake a Jihar Kano dake Arewacin Nigeria. Birnin Kano ya kasance birni na biyu mafi girma a Nigeria bayan birnin Lagos. Haka Kuma shine birni na biyu mafi yawan Jama’a bayan Lagos, domin kuwa a Kano akwai akalla mutum Miliyan bakwai.

Birnin Kano tsohon gari ne wanda aka kafa shi fiye da shekaru Dubu daya da suka wuce. Birnin ya kasance cibiyar Arewacin Nigeria wanda ake gudanar da kasuwanci da Kuma harkokin al’adun Hausawa kamar Hawan Sallah da dawakai.

 

A takaice wadannan sune Manyan Birane Guda 5 Da Suka Fi Kyau a Nigeria.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button