HausaTarihin Nigeria

Jaruman Sojoji Yan Arewa Guda Biyar a Tarihin Nigeria

Jaruman Sojoji yan Arewa

Jaruman Sojoji Yan Arewa Guda Biyar a Tarihin Nigeria. Tabbas wadannan sune Jaruman Sojoji Yan Arewa Guda Biyar a Tarihin Nigeria.

A tarihin Sojojin Nigeria yan Arewa ba’a taba samun Jaruman Sojoji kamar irin Brigadier Zakariyya Maimalari, General Murtala Muhammad, Major General T.Y. Danjuma, General Ibrahim Babangida, da Kuma General Sani Abacha.

Brigadier Zakariyya Maimalari

Brigadier Zakariyya Maimalari @tarihispace.com.ng

Brigadier Zakariyya Maimalari ya kasance kasaitaccen soja Kuma Jarumi Wanda sune zubin farko a Sojojin Nigeria daga Arewa. Ya shiga Rundunar Sojojin Nigeria a shekarar 1950 tun a lokacin tana Royal West Africa Frontier Force. Kuma yayi kwasa-kwasai a England da Kuma Amurka.

Brigadier Maimalari ya rasa ran sa ne a lokacin da Sojoji Inyamurai suka fara kaddamar da Ku na farko Wanda yayi sanadiyyar rasuwar sa tare da Manyan Yan Siyasa daga Arewacin Nigeria irin su Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto, Sir Abubakar Tafawa Balewa da sauran su. Amma kafin rasuwar sa, Maimalari yayi rawar Gani wajen kare hakkin Sojoji Yan Arewa, Wanda Hakan ne ma ya janyo ya rasa rayuwar sa.

 

General Murtala Muhammad

Murtala Muhammad

General Murtala Muhammad Jarumin Soja ne maras tsoro wanda ya taka rawar gani musamman a shekarar 1966 lokacin da ya Jagoranci Ku na ramuwar gayya akan Sojoji Inyamurai. A wannan Ku dinne ya Jagoranci kifar da Gwamnatin Soja ta General Aguiyi Ironsi.

General Murtala Muhammad ya shiga Rundunar Sojojin Nigeria a shekarar 1958. Tun a wannan lokacin General Murtala yaci gaba da bada gudunmawa ga Rundunar Sojojin Nigeria musamman wajen ganin ya taimaki Arewa. A shekarar 1966 ya Jagoranci hambarar da Gwamnatin Soja ta Aguiyi Ironsi. A shekarar 1967 zuwa 1970 Kuma ya taka rawar Gani wajen murkushe tawayen Colonel Ojukwu a Basasar Nigeria. Sai Kuma a shekarar 1975 ya Jagoranci hambarar da Gwamnatin Soja ta General Yakubu Gowon wadda a wannan lokacin ne ya zama Shugaban Nigeria na Mulkin Soja har zuwa 13 ga watan February, 1976, lokacin da wasu Sojoji Karkashin Major General Dimka Bisallah suka kashe shi.

 

Major General T.Y. Danjuma

Major General T.Y. Danjuma

Major General T.Y. Danjuma ya shiga Rundunar Sojojin Nigeria a shekarar 1960. Kuma tun a wannan lokacin yake taka rawar gani a Rundunar Sojojin gar zuwa shekarar 1979 lokacin da yayi ritaya.

Danjuma shima ya kasance gwarzon Soja Wanda ya taka rawar gani musamman a lokacin da aka kaddamar da Ku na ramuwar gayya akan Sojoji Yan Kabilar Igbo. Shine ma Wanda yaje har Ibadan ya Kamo General Aguiyi Ironsi tare da harbe shi. Ya zama Mataimakin Shugaban Gwamnatin Sojan Nigeria daga 1976 zuwa 1979 a zamanin mulkin General Olusegun Obasanjo.

General Ibrahim Babangida

General Ibrahim Babangida

General Ibrahim Babangida ya kasance Jarumin Soja wanda ya bayar da gudunmawa Mai kyau a tarihin Rundunar Sojojin Nigeria. Ya Shiga Rundunar Sojojin Nigeria a shekarar 1962.

Babangida ya taka rawar gani a tarihin Rundunar Sojojin. Misali, a shekarar 1976 lokacin da aka kashe General Murtala Muhammad, Babangida ne yaje ya yaudari Dimka Bisallah tare da Kamo shi duk da kasancewar yin hakan akwai hadari.

A shekarar 1985 yayi wa General Buhari juyin Mulki. Wanda Hakan ya bashi damar zama Shugaban Nigeria na Mulkin Soja har zuwa 1993.

General Sani Abacha

General Sani Abacha

General Sani Abacha Jarumin Soja ne maras tsoro Kuma gwanin iya mulki da tafiyar da Jama’a. Ya shiga Rundunar Sojojin Nigeria a shekarar 1963.

General Abacha ya taka rawar gani a tarihin Rundunar Sojojin Nigeria musamman a lokacin yakin Basasar Nigeria da Kuma lokacin da aka kifar da Gwamnatin Farar Hula ta Alhaji Shehu Shagari a shekarar 1983. A shekarar 1993 Kuma ya zama Shugaban Nigeria na Mulkin Soja har zuwa shekarar 1998. A lokacin Mulkin sa yayi rigima da kasashen yamma musamman Amurka. Wannan dalili ne ma yasa wasu suke ganin kasar Amurka tana da Saka hannu a mutuwar sa a shekarar 1998.

 

Kammalawa

Wadannan jerin Sojojin tabbas Sojoji ne Jarumai Wadanda a tarihi an tabbatar da jurumtakar su. Sai dai Basu kadai bane a tarihi, akwai wasu da yawa.

 

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button