HausaTarihin Mutum

Duniya Labari!!! Wai Har Janar Ibrahim Badamasi Babangida Ya Cika Shekara 81

Janar Ibrahim Babangida

Duniya Labari!!! Wai Har Janar Ibrahim Badamasi Babangida Ya Cika Shekara 81. Tabbas Duniya Labari!!! Wai Har Janar Ibrahim Badamasi Babangida Ya Cika Shekara 81.

Tsohon Shugaban Kasar Nigeria na Mulkin Soja General Ibrahim Badamasi Babangida ya cika Shekara 81 a duniya. An haifi Ibrahim Babangida ne a garin Minna na Jihar Niger a ranar 17 ga Wata August, 1941.

General Babangida ya Shiga harkar Soja a shekarar 1962 inda ya shiga Rundunar Sojojin Nigeria da matsayin Second Lieutenant. Tun daga wannan lokaci ne yake a Rundunar Sojojin Nigeria inda taka mukamai daban daban har zuwa shekarar 1993 lokacin da yayi ritaya daga Rundunar Sojojin Nigeria da matsayin General.

Babangida ya zama Shugaban Kasar Nigeria na Mulkin Soja daga shekarar 1985 zuwa 1993. A lokacin sa an samu ayyukan ci gaba sosai a Nigeria. Sai dai Kuma an samu gagarumin cin hanci da rashawa har takai wasu suna ganin a zamanin sa ne cin hanci da rashawa ya samu gindin zama a Nigeria.

Shugaba Babangida ya Auri Matar sa wato Maryam a shekarar 1969. Kuma sun kasance tare tsawon shekaru 40 har zuwa 2009 like lokacin da ALLAH YA Yi mata rasuwa. Kuma sun haifi Yaya guda 4. Tun rasuwar Maryam Babangida, Janar Babangida Bai sake yin aure ba duk da cewar kasaitattun mata sun nuna Sha’awar auren sa.

General Ibrahim Babangida tare da jikokin sa

MUNA TAYA GENERAL IBRAHIM BADAMASI BABANGIDA MURNAR CIKA SHEKARU 81 A DUNIYA 

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button