HausaLabaran Kasa

Manyan Attajiran Nigeria Guda Uku Yan Asalin Jihar Kano

Attajiran Nigeria Yan Asalin Jihar Kano

Manyan Attajiran Nigeria Guda Uku Yan Asalin Jihar Kano. Wadannan sune Manyan Attajiran Nigeria Guda Uku Yan Asalin Jihar Kano

Aliko Dangote 

Aliko Dangote

Aliko Dangote haifaffen garin Kano ne wanda ya fito daga Gidan Attajirai na Alasan Dantata. Domin kuwa kakan Dangote na wajen Mahaifiya shine Alhaji Sanusi Dantata wanda yake babban da ga Alhaji Alasan Dantata.

An haifi Dangote a Shekarar 1957 a garin Kano. Kuma a garin ya taso ya fara harkar kasuwancin sa har takai ya zama bakar fata da yafi kowa kudi a duniya.

Dangote shine Shugaban Rukunin Kamfanonin Dangote, Kuma Kudaden Dangote sun Kai kiyasin dala Biliyan da digo biyar 8.5$ . Kuma kudaden nasa sun samu ne ta hanyar hadadar Kasuwancin Kamfanoni daban daban.

 

Abdussamad Isyaka Rabiu

Abdussamad Isyaka Rabiu

Abdussamad Isyaka Rabiu shima haifaffen garin Kano ne wanda aka haifa a shekarar 1960. Mahaifin sa shine babban Malami Kuma Attajiri Sheikh Isyaka Rabiu.

Abdussamad ya kasance Shugaban Rukunin Kamfanonin BUA, Kuma shine na biyu a kudi a Nigeria. Kiyasin Kudin sa yakai kimanin dala Biliyan uku da digo biyu $3.2. Kamfanonin nasa suna samar da harkokin shinkafa, filawa, sumunti, man Fetur da sauran su.

 

Auwalu Abdullahi Rano (A.A. Rano)

Auwalu Abdullahi Rano

Auwalu Abdullahi Rano Wanda aka Fi sani da A.A. Rano ya kasance daya daga cikin manyan Attajiran Nigeria wanda suke Yan asalin Jihar Kano.

Auwalu Rano shine Shugaban Rukunin Kamfanonin A.A. Rano Nigeria Limited Wanda suke harkar hada-hadar man Fetur. Kuma Kiyasin kudin sa yake dala Biliyan biyu 2$ billion.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button