HausaLabaran Kasa

Ina Zazzagawa !!! Da Yiwuwar A Canzawa Jihar Kaduna Suna Zuwa Jihar Zazzau

Kaduna to Zazzau State

Ina Zazzagawa !!! Da Yiwuwar A Canzawa Jihar Kaduna Suna Zuwa Jihar Zazzau. Da Yiwuwar za’a canza sunan Jihar Kaduna zuwa Jihar Zazzau.

Daya daga cikin Sanatocin Jihar Kaduna ne ya Kai Kudirin zuwa ga Majalisar Dattawan Nigeria domin a Canzawa Jihar suna zuwa Jihar Zazzau. Kuma Sanatan ya bukaci ayi hakan ba tare da bata lokaci ba.

Akawun Majalisar Dattawan Nigeria ne ya tabbatar da haka ya Kuma ce matukar za’a bada hadin Kai to lamarin zai tabbata. Yan Majalisar Dattawan guda biyu da suka hada da Senator Uba Sani da Kuma Senator Abdu Kwari ne aka ce sun gabatar da Kudirin Kuma ya samu amincewar Yan Majalisar Wakilai daga Jihar Kaduna guda 13 daga cikin 15.

Majiyar mu ta tabbatar da cewa Shugaban Majalisar Dattawan Nigeria Senator Ahmad Lawan ya aikawa da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari Kudirin domin ya Saka hannu. Kuma ana Saka ran cewa Shugaban Kasar zai Saka hannu a irin kowanne lokaci.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button