HausaLabaran kannywood

Jaruma Saima Muhammad ta Caccaki Yara Masu Karyar iPhone

Saima Muhammad @tarihispace.com.ng

Jaruma Saima Muhammad ta Caccaki Yara Masu Karyar iPhone a gari. Jarumar ta caccaki yara masu karyar iPhone ne a gari.

Jarumar ta nuna takaicin ta akan yadda wasu matasa Maza da mata suke gasa wajen siyen iPhone duk dai don su burge mutane. Ta Kara da cewa wasu daga cikin matasan ko sitirar kirki Basu da ita. Wasu Kuma a gidajen iyayen su babu abincin kirki.

Maganar da Jarumar tayi Kuma akwai kamshin gaskiya domin kuwa yanzu a cikin al’umma Yara kanana sun koma suna siyen iPhone ta kowanne hali. Har takai wasu yan matan suna bayar da kan su, wasu mazan kuwa suna yin sata duk don su sayi iPhone.

Ita dai Saima Muhammad ta kasance daya daga cikin Jarumai mata na farko a Masana’antar wasan Kwaikwayo ta Kannywood wanda suka fara yin fim tun suna da jajayen Sahu. Sai dai yanzu ta fara manyanta har wasu suna ganin ta zama matashiyar Dattijuwa a harkar fim.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button