HausaLabaran Kasa

Jami’an Amotekun Sun Sun Ci Zarafin Yan Arewa a Jihar Oyo

 

Amotekun @tarihispace.com.ng

Jami’an Amotekun Sun Sun Ci Zarafin Yan Arewa a Jihar Oyo a wannan satin da muke ciki. Jami’an dai na Amotekun Sun Ci Zarafin Yan Arewan masu zuwa Jihohin Yarabawa.

Jami’an Tsaron dai sun kasance Jami’an tsaro na musamman Wanda gamayyar Jihohin Yarabawa da suka hada da Lagos, Oyo, Ogun, Osun, Ondo, da Ekiti. Wadannan Jihohin ne suka hadu domin su kawo wa yankunan su tsaro.

Jami’an Amotekun din dai sun Yi kaurin suna wajen kamawa tare da tsare yan Arewa masu zuwa Jihohin Yarabawa domin ci rani. Kuma sun bada dalilin cewa wasu Yan Arewan bata gari.

Sai dai Kuma a Arewacin Nigeria mutane suna kallon Kungiyar Amotekun a matsayin wata Kungiya da aka kirkiro domin a musgunawa Hausawa da Fulani. Kuma Hakan yana neman tabbata, domin kuwa a wannan satin Jami’an Kungiyar Tsaron sun kama yan Arewa kusan mutum dari tare da ci musu zarafi.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button