HausaLabaran kannywoodUncategorized

Ta Tabbata dan Ali Nuhu ya samu Kungiyar Kwallon Kafa a England

Ali Nuhu @tarihispace.com.ng

Ta Tabbata dan Ali Nuhu ya samu Kungiyar Kwallon Kafa a England. Ta fara fitowa fili cewa dan na Ali Nuhu ya samu Kungiyar Kwallon Kafa ta matasan Yara ne a kasar England.

Ahmad Ali Nuhu dai shine da namiji tilo da Ali Nuhu ya haifa. Wannan dalilin ne yasa Ali Nuhun yake matukar son dan sa tare da nuna masa matukar kulawa domin ganin ya cimma burin sa a rayuwa.

Tun a watan da ya gabata ne Ali Nuhu ya dauki dan nasa zuwa Kasar England domin ganin cewa an gwada basirar dan nasa Kuma wata Kungiya ta dauki shi.

Yara masu yawan gaske musamman daga Kudancin Nigeria sun samu nasarar zuwa kasar England domin a gwada basirar su tare da daukar su a matsayin yan wasa. Kuma da yawan su sukan tsallake.

Don haka ne shima Ali Nuhu ya dauki dan nasa Wanda tun tuni yake matukar son harkar Kwallon Kafa. Daga dukkanin alamu kuma burin Ahmad ya cika na buga Kwallon Kafa a rayuwar sa.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button