HausaLabaran Kasa

Sarki Sanusi Yace Bai Yi Dana Sanin Cire Shi Daga Sarkin Kano ba

Sanusi Lamido @tarihispace.com.ng

Sarki Sanusi Yace Bai Yi Dana Sanin Cire Shi Daga Sarkin Kano ba. Ya bayyana cewa shi bashi da wani takaici don an cire shi daga Sarkin Kano.

Sarkin ya bayyana haka ne a taron cikar sa shekara 61 a duniya Wanda aka gudanar a biranen Abuja da Kaduna.

Sarki Sanusi II dai shine Sarkin Kano na 14 a jerin Sarakunan Kano Fulani, Kuma na 57 a jerin Sarakunan Kano gaba ki daya. Gwamnatin Kano Karkashin Rabiu Kwankwaso ce ta nada shi a shekarar 2014 bayan rasuwar Sarkin Kano Ado Bayero.

Sai dai Kuma Kash !!!, a shekarar 2020 ne Gwamnatin Kanon Karkashin Abdullahi Ganduje ta cire shi sakamakon wasu dalilai Wanda har yanzu an kasa sanin ainahin su.

Sarki Sanusi II bashi sarki na farko da Gwamnati ta taba cirewa a Kano ba. Domin kuwa a shekarar 1963 ma Gwamnatin Jihar Arewa Karkashin Alhaji Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto ta cire kakan sa wato Sarkin Kano Sanusi I.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button