Labaran kannywood

ABALE YABAR FILM YA KOMA SOJA

Tirkashi, fitaccen dan film din dai wanda akafi wani da Abale yabar sana’ar film inda yakoma gidan soja.

Dama lokuta da dama Abalen yana nuna  shaawarsa akan cewa yanaso yazama soja inda yanzu muke gani burinsa yacika dan angansa cikin shiga irinta sojoji.

Abale kamar yadda muka sani tsohon maaikacin lafiya ne kuma ya shigo sana’ar film ne saboda sha’awa ta sana’ar da yake sosai. amma duk da haka yana nuna cewa yafison zama soja a rayuwarsa fiye da komai. hakan yasa yace sai yayi iyaka bakin kokarinsa domin ganin cewa burinsa yacika.

Alhamdullah yanzu dai burin jarumin naku yacika, sai dai yan uwa da abokan arziki ayi masa fatan gamawa lafiya. ganinsa a kayan sojoji yaja ceceku ce sosai a social media inda yan uwa da abokan arziki suke ta san barka, wasu kuma sua ganin kamar beyi dai dai ba, duba da yanayin tsaro daya shafe duk fadin kasar nan.

Hausawa kance kowa da kiwon daya karbesa, wai makocin mai awakuya yase biri, a bangaren wasu magoya bayan kuwa sunce, Abale yayi dai dai duba da kirar da Allah yayi masa sai dai dai kawai ayi masa fatan alkhairi kamar yadda aka fara cikin nasara Allah yasa agama lafiya Ameen.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button