HausaKanoMasarautar Kano

Sarautun Manyan Bayi a Masarautar Kano

Manyan Bayi a Masarautar Kano @tarihispace.com.ng

Sarautun Manyan Bayi a Masarautar Kano wasu sarautu ne da Mai Martaba Sarkin Kano yake bawa wasu daga cikin amintattun bayi wanda suka kasance cikin dinbin bayi da Sarkin Kano ya mallaka. Wadannan manyan bayi da aka bawa saurauta su ake kira da Fadawan Sarki.

BAYIN SARKI

Bawa wani mutum ne namiji ko mace da ake mallaka ta hanyar yaki, gado, kyauta, ko kuma ta misaya. Sarki yakan mallaki ne ya ajiye su a gidan sa ta dayan hanyoyin da muka ambata. Don haka wadannan bayin basu da abin dogara sai Sarki. Haka Kuma sukan yi komi ba tare da wasa ba matukar ya kasance umarnin Sarki ne ko Kuma hidimta masa. Misali, saboda kiyaye lafiya da martabar Sarki, bawa ya kwammace ya rasa rayuwar sa akan ya bari wani Abu ya samu Sarkin.

Don haka a takaice bawa da iyalan sa duk mallakar Sarki ne. Idan bawa ya rasu to iyalan sa sukan ci gaba da zama tare da hidimtawa Sarkin Kano.

FADAWAN SARKIN KANO

Fadawa sun kasance wasu amintattun bayi wanda Sarkin Kano yake janyo su kusa da shi tare da basu sarautu domin su hidimta masa a wasu ayyuka na musamman. Wadannan hidindimu da wadannan manyan amintattun bayi suke yiwa Sarkin Kano sun hada da bawa Sarki tsaro, kai-kawo tsakanin Sarki da talakawan sa, noma a gonakin Sarki, kula da cikin gidan Sarki, kula da shimfidun Sarki, kula da dawakan Sarki, da sauran su.

Sarautun da ake bawa wadannan manyan bayi Wadanda ake kira da Fadawa sun hada da Shamaki, Dan Rimi, Sallama, Sarkin Dogarai, Babban Zagi, Kilishi, da Sarkin Hatsi.

Shamakin Kano

Shamaki shine Jagoran Fadawa da kuma dukkanin bayi a Masarautar Kano. A Koda yaushe idan Sarki zai yi tafiya to tabbas zaka ga Shamaki ne akan gaba. Muhimman ayyukan Shamaki sun hada da shigar da harkokin da suka shafi kauyuka, da Kuma sauran ayyuka a gidan Sarki kamar gine-gine, da Kuma sana’o’i a.

 

Shamakin Kano

Hoton Mai Girma Shamakin Kano a kan Dokin sa ranar Hawan Sallah

Dan Rimin Kano

Dan Rimi shine babban bafade na biyu a bisa iko da girma a cikin bayin Sarkin Kano. Aikin Dan Rimi yafi karfi a wajen kula da gidajen Sarki na waje kamar Nassarawa, Dorayi, da Fanisau. Haka Kuma yana kula da gonaki da gandun Sarki dake a gurare daban daban a Kasar Kano.

Sallaman Kano

Sallama shine na uku a jerin Fadawan Sarki masu iko. Shine wanda ke yiwa duk Mai bukatar ganin Sarkin Kano iso, da Kuma kula da dukkanin kyaututtukan da Sarki ke yi ko Kuma ake Yi masa. A takaice dai Sallama shine Mai kula da shige da ficen Jama’a a gidan Sarki. Sallama baya barin fada ko da kuwa Sarki yana gida ko ya bar gari.

Shamakin Kano @tarihispace.com.ng

Hoton Mai Girma Sallaman Kano

Sarkin Dogarai

Sarkin Dogarai shine kamar babban Jami’in tsaro na Sarkin Kano. Akwai Dogarai da yawa a Karkashin sa wanda aikin sune kula da tsaron Sarki tare da dukkanin sauran tsaro a gidan Sarki. Sarkin Dogarai ne Kuma ke taimakawa Sarki hawa bisa Doki da Kuma sauka daga dokin.

Sarkin Dogaran Kano@tarihispace.com.ng

Mai Girma Sarkin Dogaran Kano

Babban Zagi

Babban Zagi shine yake ratayawa dokin Sarki sirdi da jar alkyabba. Haka Kuma shike rikewa Sarki linzamin Doki har sai ya hau ya zauna daidai. A zaman fada kuwa shine yake zaune dab da karagar Sarki rike da Tagwayen Masu.

Kilishi

Kilishi ya kasance babban bafade wanda yake kula da shimfidar Sarki. Aikin sa ne ya baza kilisai lokacin zaman fada da Kuma made su a lokacin da zaman fada ya kare. Haka Kuma idan an nada dagaci to Kilishi ne yake riko hannun sa tare da kawo shi gaban Sarki.

Sarkin Hatsi

Sarkin Hatsi ya kasance babban bafade wanda yake kula da harkar abinci a gidan Sarki. Sarkin Hatsi ne Kuma ke kula da duk wata zakkah ko kyautar abinci wadda Sarki ke yi ga Al’umma. Haka Kuma a lokacin Sallah Babba Sarkin Hatsi ne yake akan sha’anin ragon da Sarki zai yanke.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button