HausaKano

Al’adu da Bukukuwa a Kano

The image include the image of Emir of Kano, President Buhari, and Kano wedding picture of Bride and groom

Al’adu da Bukukuwa a Kano ya kasance muhimmin al’mari wanda yake nuna al’adun Hausa musamman a Kano. Tun kafin Kanawa su cudanya da wasu kabilun suna al’adun su na gado, wanda suke gudanar da rayuwar su a Kai.

Sassan dabi’u da al’adun Kanawa sun hada da yanayin muhallin su, sana’o’in su, da nau’in abincin su, da suturun su, da sauran harkokin su na aure da haihuwa.

HARSHEN HAUSA

Harshe ko yare shine hanyar sadarwa ta farko tsakanin yan Adam. Shine babbar hanya da take tabbatar da al’adun mutane. Haka Kuma shine Babbar hanya wadda take kullawa tare da kyautata zumunci, tattalin arziki, addini, siyasa, da sauran hanyoyin rayuwa.

Don haka Kanawa sun kasance Wani sashi na al’ummar Hausawa wanda suke amfani da harshen Hausa wajen sadarwa da isar da sakonni tsakanin junan su da Kuma sauran Yan uwan su na kasar Hausa kamar Katsinawa, Zazzagawa, Gobirawa, da Kuma sauran kabilu masu amfani da harshen Hausa.

ABINCI DA SUTURA

Dangane da abinci da Kuma sutura, Kanawa na da ire-iren abincin su da suka danganci kayan amfanin gona ko yayan bishiyoyi. Daga ire-iren abincin akwai gero wanda ake yin tuwon sa, dambu, fura da sauran su. Haka Kuma akwai dawa, maiwa, masara, wake, rama, zogale, tafasa da sauran su.

Haka Kuma duk fadin kasar Hausa, Kano ce gari mafi shahara da ake samar da gurasa har ta kai ma ana cewa Kano garin gurasa. Koda yake gurasa asalin ta abincin Larabawa ne, amma sakamakon alakar addini da kasuwanci tsakanin Kano da kasashen Larabawa na Arewacin Africa tasa gurasa tazo Kano fiye da shekara Dari biyar. Ana sarrafa gurasa da kuli-kuli da man gyada wanda ake kiran hadin bandashe.

Hoton gurasa @tarihispace.com.ng

SUTURA
Kanawa na amfani da sutura daban daban Kuma wanda suke nuna cewa lallai mutumin da ya Saka su Bahaushe ne wanda yake daga Kano. Daga cikin suturar Maza a Kano akwai babbar riga (sace, shakwara, garo, ko aganiya) da wando (buje, tsala, ko kwarjalle), da Kuma hula mafi yawanci wadda ake kiran ta da habar kada. Haka wasu musamman masu sarauta da malamai suna saka rawani.

Mata Kuma suna Saka zani (bakurde, saki, bunu, tsamiya, mudukare, ko gansarki), da Kuma riga (mudukare ko riga mai hannu), da dankwali (saro ko fatala).

Shigar Hausa a Kano

Hoton Suturar Hausawa a Kano

BUKUKUWA

Bukukuwan da ake yi a Kano suna da dama wanda ake gudanar da su bisa al’adar Hausa. Akwai bukukuwan da Kanawa suke yi tun ainihi kafin zuwan addinin Musulunci, da kuma wanda suka samu bayan zuwan addinin Musulunci.

Bukukuwan Kanawa wadanda suka samo asali tun kafin zuwan Musulunci sune irin su bikin Kalankuwa, Bikin Shan Kabewa, Bikin Suna, Bikin Aure, da kuma Bikin Mutuwa.

Bukukuwan da suka samo asali bayan zuwan addinin Musulunci Kuma sune irin Bikin Karamar Sallah da Babbar Sallah, Bikin Maulidi, Bikin Takutaha, Bikin Saukar Al’qurani.

Sai dai Kuma a duk cikin bukukuwan da ake yi Kano babu kamar bukukuwan Karamar Sallah da Babbar Sallah. Bikin Karamar Sallah ana yin sane a farkon ranar watan Shawwal, sai Kuma Babbar Sallah wadda ake yi a ranar goma ga watan Zul Hijja. A wadannan lokacin bukukuwan Sarkin Kano yakan gabatar da haye-hayen dawaki tare da mahaya domin gaisawa da Al’ummar Kanawa. A lokacin hawan Sallah da Mai Martaba Sarkin Kano yake jagoranta dukkanin Hakimai da Dagatai na fadin kasar Kano sukan shigo birnin Kano domin yin haye-hayen Sallah tsawon kwana biyar. Akwai ire-iren Hawan Sallah a Kano guda hudu kamar haka:

  1. Hawan Ranar Idi (a kowacce Karama da Babbar Sallah)
  2. Hawan Daushe (a kowacce karama da Babbar Sallah)
  3. Hawan Nasarawa ( a kowacce karama da Babbar Sallah)
  4. Hawan Dorayi (a Karamar Sallah kawai)
  5. Hawan Fanisau (a Babbar Sallah kawai)

HOTUNAN HAWAN SALLAH A KANO

Sarkin Kano Hawan Sallah

Hoton Maimartaba Sarkin Kano a ranar Hawan Babbar Sallah

Sarkin Kano

Hoton Maimartaba Sarkin Kano a lokacin Hawan Daushe

Hawan Sallah Kano

Mahayen Kano a ranar Hawan Nasarawa

Lifidan Kano

Lifidan Kano

 

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button