Labaran kannywood

Bazan taba mantawa da kyautar motar da Ali Nuhu yayi min ba inji shamsu dan iya

Bazan taba mantawa da kyautar motar da Ali Nuhu yayi min ba inji shamsu dan iya

Jarumi acikin masana’antar shirya finafinai mai suna shamsu Dan Iya ya kasance yaron Ali Nuhu ne tun fil azal wanda kuma Ali Nuhu ne sanadiyyar shigarsa harkar film kuma ya dafa masa har yayi suna

Ya baiyana cewa abinda bazai taba mantawa ba a rayuwarsa shine kyautar motar Ali Nuhu ya bashi shine abinda bazai taba mantawa ba inda yace da wanda ya baka mota da wanda ya kaika Saudiya babu ta yadda za ayi ka manta da wayan nan mutum biyun

Sai dai wasu naganin to ai daman irin wahalar da yayi masa dole bazai barshi hakakaba yana yawo ba tare da motaba inda wasu kuma sukace duk da hakan Ali Nuhun yayai kokari tunda anga nawane acikin kannywood suke da yara amma basu temakesu da komai ba

Acikin bidiyon anga tsaleliyar motar wacce kowa yaganga yasan a zuba kudi kafin asiyeta bawai mota ce me araha ba motace me kyau kuma ta yayi

Inda wasu ke ganin ai shima shamsu dadewar sa a kannywood ya kamata shima ace ya siyi mota da kudin amma kuma ya jira har sai da me gidansa ya siya masa yace to ai hakan ba laifi bane tunda dai me gida nane ya siyamin da ace wanine shine zai zama abin magana

Ali dai shine jarumin da yafi kowanne jarumi suna da kuma kudi da dadewa acikin masana’antar kannywood kuma wanda yafi kowa iya acting acikin shirin Film sannan shine mai kamfanin FKD saboda dadewarsa acikin harkar ne yasa yafi kowa suna da kuma samun kuɗi acikin sana’ar

Anasa bangaren shima shamsi dan Hajiya ya baiyana jin dadinsa akan motar da megidan nasa Ali Nuhu ya bashi inda yayi masa addu’ar Allah ya kara budi

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button