HausaHausa

TARIHIN ASALIN HAUSAWA

A map showing the extent of Hausaland. Source : creativecommons.org

Tarihin Asalin Hausawa ya kasance babban al’amari wanda yake bukatar nutsuwa sosai. Hausawa sun kasance wata al’ummar bakaken fata wadda take zaune a yankin arewacin Nigeria ta yanzu da kuma kudancin kasar Niger ta yanzu. Hausawa sun kasance suna yin magana da harshen Hausa wanda yake daya daga cikin mafi yaduwar harsunan bakaken fatar Arewa.

Haka kuma Hausawa sun kasance al’umma masu kwazo wadanda suka shahara da yin fatauci da kuma yin kasuwanci. Sannan kuma akalla kaso 95% na al’ummar Hausawa musulmi ne masu bin addinin musulunci.

Asalin Hausawa

An samu sabani akan Tarihin Asalin Hausawa tsakanin malamai da dama masu nazarın asalin Hausawa na tarihi da rubuta shi, da kuma masu tarihin baka mafi dadewa da tasiri na Tarihin baka na Bayajidda mijin Sarauniya Daurama.

Don haka ne aka samu bayanai daban-daban akan tarihin asalin Hausawa. Ga wasu daga cikin bayanan :

HAUSAWA DAGA MISRA SUKE

Wasu daga cikin masana masu binciken tarihin kasar Hausa sun alakanta tarihin asalin Hausawa da yankin Mısra wato kasashen da suka hada da kasashen Egypt, arewacin Sudan, Libya, da kuma Palestine na yanzu.

Daya daga cikin manazartan wato Lugard a cikin littafin sa ‘A Tropical Dependency’ yace Hausawa sun fito be daga cikin kabilar Kibdawan Misra. Ya Kuma kara da cewa Hausawa da harshen su sun samo asali ne daga suna Fir’auna Hausal kakan Fir’auna Namarudu.

HAUSAWA DAGA HABASHA SUKE

Wasu Kuma daga cikin masana tarihi wadanda suka nazarci tarihin asalin Hausawa sun ce Hausawa sun fito ne daga yankin Habasha wato kasar Ethiopia a yanzu.

Masana da suka samar da wannan bayani sun ce kabilar Hausawa na farko da suka sauka a yankin kasar Hausa sun kasance maharba ne wadanda ake ganin sun taso ne da yankin gabashin Africa musamman yankin Habasha. Manazartan sun ce al’adun Hausawan farko musamman ta bangaren addini, sutura, da kuma wasu kalmomi harshe sun kasance suna da kamanceceniya da na wasu mutanen yankin Habasha. Misali, kabilun Hausawa na farko sun kasance suna bautawa rana wanda ya kasance addinin da mutanen Habasha suka fi shahara akan sa.

LABARIN BAKA NA BAYAJIDDA

Wannan labarin baka na Bayajidda ya nuna cewa tarihin asalin Hausawa ya samo asali ne daga wani mutumi mai suna Abu-Yazidu wanda aka fi sani da Bayajidda. Labarin ya nuna cewa shi Bayajidda ya kasance dan Sarkin Bagadaza. An ce Bayajidda yayi rigima da mahaifin sa ne wanda ya sa dole yayi hijra zuwa yamma tare da wasu daga cikin mabiyan sa.

Kafin zuwan Bayajidda kasar Hausa, sai da ya sauka kasar Borno inda ya auri yar sarkin Bornon mai suna Magira. Sai dai daga Sarkin Borno ya nemi ya hallaka shi, don haka ya tare da Magira. Da suka zo wani gari mai suna Garun-Gabas sai matar sa Magira ta haihu, don haka ya bar ta anan ya kara gaba. Daga karshe, Bayajidda ya sauka a Daura inda ya nuna bajinta na kashe wata macijiya wadda ta addabi al’ummar garin. Saboda wannan bajintar, yasa Sarauniyar Daura mai suna Daurama ta aure shi. An ce sun haifi da Mai suna Bawo wanda shi kuma ya haifi yaya guda shida wadanda suka kafa Masarautun kasar Hausa wadanda ake kira da Hausa Bakwai kamar haka :

  1. Bagauda a Kano
  2. Kumayo a Katsina
  3. Gunguma a Zazzau
  4. Uban Doma a Gobir
  5. Gazori a Daura
  6. Zaman Kogo a Rano
  7. Zauna Gari a Birom (Garun-Gabas)

Sai dai Kuma manyan masana Tarihin Asalin Hausawa sun bayyana labarin Bayajidda a matsayin tatsuniya. Misali, manazartan sun tabayi cewa shin mutanen da Bayajidda ya tarar a Daura wane harshe suke amfani da shi ?. Daga karshe manazartan sun ce labarin Bayajidda zai iya samun gindin zama da karbuwa ne kawai a matsayin Tarihin kafa Masarautun kasar Hausa.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Check Also
Close
Back to top button