JUYIN-JUYA HALIN KASAR IRAN

A History and Culture Hub

JUYIN-JUYA HALIN KASAR IRAN

Wasu daga cikin yan gwagwarmaya a lokacin Juyin-Juya Halin Kasar Iran. Source : wikimedia.org

Juyin-Juya Halin Kasar Iran wani kokari ne da yan kasar Iran suka yi wanda ya basu nasarar hambarar da mulkin sarauta a kasar tare da kafa mulkin jamhuriyar musulunci ta Iran. A karkashin Juyin-Juya Halin, al’ummar kasar su hambare mulkin Sarki Shah Muhammad Reza Pahlavi tare da nada Ayatollah Ruhollah Khomeini a matsayin jagoran kasar.

An kwashe kimanin shekara daya a gudanar da gwagwarmayar Juyin-Juya Halin Kasar Iran wato daga farkon shekarar 1978 zuwa farkon shekarar 1979.

Asalin Juyin-Juya Halin

Kafin faruwar Juyin-Juya Halin Kasar Iran, abubuwa da yawa sun faru wadanda suka janyo Juyin-Juya Halin. Sai dai mafi muhimmanci shine dalili na addini. Domin kuwa mutanen kasar Iran sun kasance mutane masu kishin addini da kyamatar akidun kasashen Yamma.

A cikin shekarar Shekarar 1963, gwamnatin Masarautar Iran karkashin Sarki Shah Pahlavi ta kaddamar da shirin gwamnati akan tattalin arziki, tsarin siyasa, da kuma tsarin zamantakewar al’umma wanda ake kira da ‘White Revolution’. A karkashin tsarin na White Revolution, Sarki Shah ya tsara cewa daga wannan lokacin kasar Iran zata dinga salon tsarin tattalin arziki, siyasa, da kuma zamantakewa irin na kasashen Turawan Yamma da Amurka. Sai dai kuma mutanen kasar Iran sun nuna adawar su ga wannan tsarin saboda sun ce tsari ne wanda yaci karo da addinin Musulunci da kuma al’adunsu. Don haka ne tun daga nan gwamnatin Masarautar Iran ta fara yin rigima da malaman addini da kuma sauran yan kasa.

Haka kuma zuwa tsakiyar shekarun 1970 kasar Iran ta fara fuskantar matsain tattalin arziki. Don haka ne masana masu ilmi, dalibai yan gwagwarmaya, da kuma matsakaitan yan kasuwa suka fara juya wa gwamnati baya. A kwana a tashi ma’aikata suka fara tafiya yajin aiki, wasu daga cikin al’ummar kasar kuma suka fara zanga-zanga. Hakan kuma ya fara alamta cewa akwai yiwuwar faruwar hargitsi a kasar Iran.

Faruwar Juyin-Juya Halin Kasar Iran

Gwagwarmayar Juyin-Juya Halin Kasar Iran ya fara ne a farkon shekarar 1978 a lokacin da dubban al’ummar kasar Iran suka fara zanga-zangar kin jinin gwamnatin Masarautar Iran. A hannu daya kuma Shugaban Addinin Musulunci na Iran wato Ayatollah Ruhollah Khomeini wanda yake gudun hijra a kasar Iran yayi amfani da damar wajen bawa yan gwagwarmayar kwarin gwiwa ta hanyar yin jawabai da taimakon kudi.

Zuwa watan December na shekarar 1978 miliyoyin yan kasar Iran sun cika manyan titutuna na babban birnin kasar wato Tehran da kuma sauran manyan biranen kasar. Mutanen kasar sun nuna gajiyawar su ga gwamnatin Sarauta tare da bukatar Sarkin Iran Muhammad Reza Pahlavi da ya sauka daga mulki. Don haka ne a farkon shekarar 1979 Sarki Shah ya gudu ya bar kasar Iran tare da yin gudun hijra zuwa kasar Masar wato Egypt. Hakan kuma ya kawo karshen Juyin-Juya Halin Kasar Iran.

A daya hannun kuma mutanen kasar Iran sun gayyaci Ayatollah Ruhollah Khomeini domin ya dawo ya kafa gwamnatin Musulunci. Don haka ne Ayatollah ya dawa kuma ya zama sabon jagoran kasar Iran wadda ta koma Jamhuriyar Musulunci ta Iran wato a turance Islamic Republic of Iran.

 

Leave a Reply

Your email address will not be published.