HausaMasarautar Kano

ZUWAN TURAWA KANO

Kofar Shiga Gidan Rumfa wato Fadar Masarautar Kano. Source : creativecommons.org

Zuwan Turawa Kano ya kasance wani lokaci wanda Turawan Ingila (Britain) suka samu nasarar mamaye kasar Kano tare da kafa mulkin mallaka a shekarar 1903.

Asalin Zuwan Turawa Kano

Zuwa shekarar 1900 Turawan Ingila sun mamaye kusan daukacin Masarautu dake karkashin Daular Sokoto. Daga cikin manyan da suka gagara a mamaye su sun kasance Kano da Sokoto. Don haka ne Gwamnatin Mulkin Mallaka ta Ingila ta himmatu wajen ganin sun mamaye Kano da Sokoto.

Ana cikin wannan halin ne aka samu aukuwar wani lamari wanda ya fusata Ingila har taci alwashin sai ta cinye Kano da Sokoto. Wannan lamari kuwa ya faru ne a Keffi inda Magajin Garin Keffi Ibrahim Danyamusa ya kashe wani bature mai suna Kaftin Maloney wanda ya kasance Razdan din Keffi. Don haka ne shi Magaji Danyamusa ya gudu zuwa arewa har ya iso Kano inda Sarkin Kano Alu Maisango ya tarbe shi da girmamawa. Wannan tarba da Sarkin Kano Alu yayi wa Magajin Garin Keffi ya janyo Gwamnatin Mulkin Mallaka ta Ingila a Nigeria karkashin Janar Lord Lugard ta umarci rundunar soja domin mamaye Kano da Sokoto.

Mamayar Kano

A ranar 29 ga January, 1903, sojojin Ingila kimanin guda dubu karkashin jagorancin Kanar Thomas Morland suka bar Zaria suka nufo Kano. Bayan tafiyar kwana daya sojojin suka shigo kasar Kano inda suka hadu da tarnaki a wani kauyen Kano mai suna Bebeji. Ance lokacin Sarkin Fulanin Bebeji wanda ya kasance daya daga cikin manyan jaruman Sarkin Kano ya tare sojojin domin hana su wucewa zuwa Kano. Sai dai a cikin dan kankanin lokaci sojojin Ingila suka kashe Sarkin Fulanin Bebeji tare da fasa gayyar sa.

A hannu daya kuma, kafin sojojin Ingila su tunkaro birnin Kano, tuni dama Sarkin Kano Alu Maisango ya tafi ziyara zuwa Sokoto. Saboda haka Turawa sun samu jin dadin cewa Sarkin Kano baya gari don haka za su ci Kano da dadin rai.

A ranar 2 ga February, 1903, sojojin Ingila suka iso bakin ganuwar birnin Kano tsakanin Kofar Dukawuya zuwa Kofar Kabuga. Sai dai ance turawan sun yi kokarin balle Kofar Kabuga amma taki balluwa. Don haka ne suka dawo Kofar Dukawuya inda suka yi amfani da bindigar mashingon (machine gun) tare da balle Kofar. Daga nan suka shiga cikin birnin Kano inda mutanen cikin birni suka dinga gudu suna ihu suna fadar cewa ‘nasara yaci Kano’. Su kuma sojojin sai suka nufi gidan sarki. Da isar su gidan sarki sai wasu daga cikin mayakan Sarkin Kano wadanda aka barwa jiran gari karkashin jagorancin Sallaman Kano Jatau suka tunkure su domin hana su shiga gidan sarki. Sai dai kash !, sojojin Ingila sun yi amfani da bindigogi har suka ci karumin mayakan Kano. Wannan nasara ta bawa sojojin Ingila damar shiga gidan Sarkin Kano tare da kafa tutar Ingila wadda hakan yake nufin Kano ta dawo karkashin Ingila.

Turawa sun nada sabon Sarkin Kano

Tuni bayan da Turawan Ingila suka ci Kano, Sarkin Kano Alu Maisango ya samu labari. Don haka ne yayi shawara tare da tafiya zuwa Sudan domin neman taimakon Mahdi wanda ya gagari Turawan Ingila kafa mulkin mallaka a Sudan. Sai dai kash kafin yayi nisa wasu daga cikin sojojin Ingila suka kama shi tare da kai shi Lokoja inda suka ajiye shi har ALLAH YA karbi rayuwar sa a shekarar 1926.

A wani bangaren kuma, a watan April na shekarar 1903 Turawa sun nada sabon Sarkin Kano wato Wamban Kano Abbas. Shi sabon Sarkin Kano Abbas ya kasance kamar Alu shima da ne ga Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi kuma jika ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button