HausaMasarautar Kano

YAKIN BASASAR KANO

Kofar Shiga Gidan Rumfa, Fadar Masarautar Kano. Source : creativecommons.org

Yakin Basasar Kano wani yaki ne da ya faru a tarihin Kasar Kano a tsakanin yan biyu jikokin Sarkin Kano Ibrahim Dabo akan kujerar Sarautar Kano. Wadannan yan uwa sune Sarkin Kano Tukur da kuma Galadiman Kano Yusufu. Yakin Basasar Kano ya afku a cikin shekarar 1893, kuma an kare shi a farkon shekarar 1894 lokacin da Sarkin Tukur ya rasa ran sa a yakin. Bayan rasuwar tasa kuma Alu ya zama sabon Sarkin Kano.

Dalilin Yakin Basasar Kano

An ce dalilin da ya janyo Yakin Basasar Kano ya kasance karya alkawari da aka yi wa Galadiman Kano Yusufu na zama Sarkin Kano. Shi Galadima Yusufu ya kasance babban dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi. Saboda haka bayan rasuwar Sarkin Kano Maje-Karofi mafi a cikin shekarar 1883, mafi yawan mutanen Kano sun fi son Yusufu ya gaje shi. To amma sai Sarkin Musulmi Umaru ya zabi wan mahaifin sa wato Turakin Kano Bello a matsayin Sarkin Kano. Don haka ya bawa Galadima Yusufu hakuri akan cewa idan Bello ya rasu to shi za’a nada Sarkin Kano.

Bayan kusan shekara goma, a cikin shekarar 1893 sai ALLAH YA yiwa Sarkin Kano Bello rasuwa. Saboda haka mutanen Kano suka yi ta murna cewa lokaci yayi da Galadiman Kano Yusufu zai zama Sarkin Kano. To amma kash !, maimakon haka sai Sarkin Musulmi Abdurrahman Danyen Kasko ya zabi babban dan Sarkin Kano Bello wato Tukur a matsayin Sarki. Don haka ne wannan dalili ya janyo tawaye a Kano wadda tasa Galadima Yusufu tare da magoya bayan sa suka yi sansani a Takai da Garko domin yakar Sarkin Kano Tukur.

A kwana a tashi Galadiman Kano Yusufu ya sami isassun mayaka daga sauran sassan Kasar Kano tare da kuma sauran makwabtan Masarautu irin su Ningi da Gumel. Sai dai kash !, kafin mayakan Galadima Yusufu wadanda ake kira da Yusufawa su tunkaro birnin Kano sai ALLAH YA yiwa Galadima rasuwa. Saboda haka aka nada kanin sa mai suna Alu domin ya jagoranci yakin.

An gwabza Yakin

Bayan rundunar Yusufawa sun nada Alu a matsayin jagoran su, sai kuma suka nufo Kano daga Garko domin yakar Sarkin Kano Tukur. A hanya mayakan Yusufawa suka dinga cin garuruwan dagatan Sarkin Kano wadanda suka ki yi musu mubayi’a.

Bayan kwanaki Yusufawa suka iso bakin ganuwar Kano kuma suka yi sansani a Fagge. Sai dai kuma kafin su karaso tuni Sarkin Kano Tukur ya shirya rundunar yaki domin fafatawa a wannan Yakin Basasar Kano. Washegari Sarki Tukur tare da rundunar sa wadda aka kira da Tukurawa suka fito suka hadu da mayakan Yusufawa karkashin Alu. Yaki ya kaure har zuwa la’asar lokacin da Yusufawa suka ci galaba akan mayakan Sarkin Kano Tukur. Wannan dalili ne yasa Sarki Tukur ya gudu ya bar Kano tare da wasu daga cikin mayakan sa. Sai dai mayakan Yusufawa sun bishi har zuwa iyakar kasar Kano da Katsina a wani gari da ake cewa Tafashiya inda aka sake buga wani dan karamin wanda a nan ne Sarkin Kano Tukur ya rasa ransa, kuma Yakin Basasar Kano yazo karshe.

Alu ya zama Sarkin Kano

Bayan mayakan Yusufawa sun sami nasarar tunbuke Sarki Kano Tukur daga karagar mulki sai kuma masu zabar Sarki suka zabi Alu a matsayin sabon Sarkin Kano. Shi Alu wanda ya samu sunan ‘Maisango’ saboda amfani da bindigar sango a yake-yaken sa ya kasance dan Sarkin Kano Abdullahi Maje-Karofi. Haka kuma mahaifiyar sa ta kasance ya ce ga Sarkin Musulmi Alu Babba, don haka ne ma yaci sunan ‘Alu’.

Sarkin Kano Alu Maisango ya rasa mulkin sa ne bayan Zuwan Turawa Kano a shekarar 1903.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button