HausaTarihin Africa/Turai

TARON BERLIN (BERLIN CONFERENCE)

Shugabannin Taron Berlin yayin tattaunawa. Source : kids.kiddle.co

Taron Berlin wanda a tarihance kuma a turance ake kira da ‘Berlin Conference‘ ya kasance wani taro wanda manyan kasashen Turai (European countries) suka gudanar domin tattauna yadda za su samu damar samun ikon mamaye nahiyar Africa. An gudanar da Taron Berlin a tsakanin watan Nuwamba na shekarar 1884 zuwa watan Janairun shekarar 1885.

A Taron Berlin kasashen Turai sun tattauna yadda za su mamaye tare da raba nahiyar Africa zuwa karkashin ikon su. Don haka ne tun daga taron ne kasashen Turai suka himmatu wajen mamayar nahiyar Africa ta hanyoyi daban-daban ciki har da yin amfani da karfin soja.

Kasashen da suka hadu suka gudanar da Taron Berlin a birnin Berlin dake kasar Jamus (Germany) sun hada da Great Britain, France, Germany, Portugal, Belgium, the Netherlands, Spain, Italy, Austria-Hungary, Sweden-Norway, Russia, Turkey, da kasar Amurka (United States) a matsayin mai sa ido.

Asalin Taron Berlin

Kafin gudanar da Taron Berlin a shekarar 1884, kasashen Turawa sun kasance sun mallaki kaso kaso 20% ne na nahiyar Africa. Kuma wadannan yankunan Africa da Turawa suka kafa mulkin mallaka sun kasance yankunan da suke gabar teku. Wannan dalili ne yasa kasashen Turawa irin su Ingila, Faransa, Portugal, Jamus (Germany), da sauran su suka dauki nauyin masana kimiyyar kasa wato geographers a turance domin su shiga cikin nahiyar Africa domin su gano yadda sirrin cikin nahiyar yake. Don haka ne zuwa shekarar 1870, kasashen Turawa sun sami muhimman bayanai akan yadda Africa take da kuma yadda za su mallake ta. Daga bisani kasashen Turawa suka dinga ayyana yankunan nahiyar Africa a matsayin mallakar su.

Rige-rige da kokarin mallakar yankuna masu arziki a nahiyar Africa a tsakanin kasashen Turawa ya janyo cece-kuce da takaddama a tsakanin kasashen na Turawa. Don haka ne kasar Portugal tare da shugaban Jamus mai suna Otto Von Bismarck suka tattauna tare da gayyatar sauran yan uwan su kasashen Turawa domin tattaunawa akan yadda za su raba nahiyar Africa a tsakanin su. Wannan dalili ne ya janyo yin Taron Berlin a tsakanin watan Nuwamba na shekarar 1884 zuwa watan Fabrairu na shekarar 1885 a birnin Berlin dake kasar Jamus wato Germany.

Matsayar da aka cimma a Taron

A yayin gudanar da Taron Berlin an gudanar da muhawara a tsakanin kasashen Turawa bisa jagorancin kasashen Ingila (Great Britain), Jamus, Faransa (France), da kuma Portugal. daga karshe Taron ya cimma matsaya akan yadda kasashen za su mallaki nahiyar Africa kamar haka :

  • Duk kasar da ta mamayi wani yanki na Africa to dole ne ta sanar da sauran kasashe wanda suka halarci wannan Taro na Berlin domin gujewa rigima.
  • Duk kasar da ta mamayi wani yanki na nahiyar Africa to dole ne ta tabbatar da kafa tutar ta wanda zai nuna cewa wannan yanki yana karkashin ikon ta.
  • Haka kuma an cimma matsaya cewa kogin Congo (Congo River), da kuma kogin Naija (River Niger) za su kasance a matsayin wanda ba mallakin kowa wato kowa ce kasa zata iya ratsawa ta ciki.

Saboda haka ne bayan kammala Taron Berlin, sai manyan kasashen Turai suka himmatu wajen ganin sun mallaki yankuna a nahiyar Africa domin yi musu mulkin mallaka.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button