HausaMasarautar Kano

YAKE-YAKEN SARKIN KANO DABO

Tambarin Masarautar Kano. Source : Kano Emirate Council

Yake-Yaken Sarkin Kano Dabo sun kasance wasu yake-yake ya kaddamar domin tabbatar mulkin sa da kuma kasaitar Kasar Kano. Sarkin Kano Dabo ko Ibrahim Dabo ya kasance Sarkin Kano wanda wasu suke ganin cewa yafi kowane Sarki tasiri a jerin Sarakunan Kano guda hamsin da bakwai. Dalilai da yawa kuwa sune suka hadu suka bawa Sarkin Kano Ibrahim Dabo matsayi na musamman a jerin Sarakunan Kano. Babba ko kuma daya daga cikin dalilan kuwa shine kasancewar Sarkin Kano Dabo kasaitaccen mayaki kuma wanda ya gwabza yake-yake musamman domin tabbatar da Masarautar Kano a matsayin Masarauta daya sakamakon tawaye da ya fuskanta a farkon hawan sa gadon Sarautar Kano.

Don haka ne Yake-yaken Sarkin Kano Dabo suka kasance wasu muhimman abubuwa da suka faru a tarihin Kasar Kano wanda suke bukatar a dinga tunawa da su.

Yan Tawaye a Farkon Sarautar Sa

Bayan da Sarkin Kano Sulaimanu ya rasu a shekarar 1819, sai masu bukatar zama sarakunan Kano suka bayyana tare da nuna bukatar su. Wasu daga cikin masu son sarautar Kano a lokacin sun hada da wanda sun kasance shugabannin kaddamar da Jihadi a Kano. Misali, shugaban Kabilar Fulani Dambazawa wato Malam Inusa Dabon Dambazau da kuma Malam Mandikko shugaban Kabilar Fulani Jobawa duk sun nemi a basu Sarautar Kano amma ance Sarkin Musulmi Muhammad Bello ya tsallake su tare da nada Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano saboda ilmin addini da shi Dabon yake da shi.

Sai dai ance nadin da Sarkin Musulmi ya yi wa Ibrahim Dabo a matsayin Sarkin Kano ya bata wa wadannan manya da sauran wasu a gefe rai. Saboda haka wasu daga ciki suka fara yin kokarin tawaye. Don haka ne a kokarin sa na dinki barakar dake kokarin bayyana, Sarkin Kano Dabo ya aikawa da dukkanin dagatan Kasar Kano tare da makwabtan Sarakuna wasika yana sanar da su kasantuwar a matsayin Sarkin Kano. Sai dai ance a lokacin da takardar Sarkin Kano Ibrahim Dabo ta ishe daya daga cikin manyan dagatan Kasar Kano wato Sarkin Fulanin Arewacin Kano kuma Sarkin Fulanin Dambatta Shugaban Kabilar Fulani Yarimawa wato Malam Usman Dantunku sai ya yaga takardar tare da cewa shi ba zai yiwa Sarkin Kano Dabo mubayi’a ba. Sarkin Fulanin Arewacin Kano Malam Usman Dantunku ya kara da cewa idan har ba Malam Jibir Shugaban Kabilar Fulani Yolawa aka bawa Sarkin Kano ba to shi ba zai bi kowa ba a cikin Kanawa, sai dai yaci gashin kan sa. Don haka ne ma Malam Usman Dantunku ya ayyana ballewar Arewacin Kano daga karkashin ikon Sarkin Kano (wato a turance secession) tare da ayyana kan sa a matsayin Sarki mai cin gashin kan sa.

Yakin Tawayen Dantunku

A jerin Yake-yaken Sarkin Kano Dabo babu yakin da yafi bashi wahala tare da daukar lokaci ana fafatawa irin yakin da suka gwabza tsakanin mayakan sa da na Sarkin Fulanin Arewacin Kano Malam Usman Dantunku Shugaban Kabilar Fulani Yarimawa. Domin kuwa ance an kwashe akalla kusan shekaru hudu ana fafatawa.

Abin da ya faru shine cewa lokacin da Ibrahim Dabo ya zama Sarkin Kano a shekarar 1819, Usman Dantunku yaki yin mubayi’a. Daga karshe ma sai Dantunku ya ayyana cewa shifa yanzu gashin kan sa zai ci a matsayin Sarki me zaman kan sa. Wannan dalili ne yasa Sarkin Kano Ibrahim Dabo ya ayyana yaki akan Dantunku. An kwashe shekaru ana buga yaki domin murkushe tawayen Dantunku. Sarkin Kano bai sami nasara ba har sai wajejen shekarar 1824 lokacin da Dantunku ya gudu zuwa arewa tare da mabiyan sa.

Sauran Yake-Yake

Bayan da Sarkin Kano Dabo ya samu nasara akan Dantunku, sai ya jiya hankalin sa zuwa sauran yan tawaye a fadin Kasar Kano.

YAKIN SANKARA

Kafin mu bada labarin nan zamu so me karatu ya fahimci cewa Masarauta ko Kasar Kano ta kasance kasa me fadi. Saboda haka ne lokacin da Sarkin Kano Dabo ya zama Sarkin Kano aka samu tawaye da yawa.

Lokacin da Sarkin Kano Dabo ya zama Sarkin Kano, shima Sarkin Fulanin Sankara mai suna Ardo Hunturbe yaki yin mubayi’a ga Sarki Dabo. Don haka ne a shekarar 1825 Sarkin Kano Dabo ya nufi garin Sankara domin murkushe tawayen Sarkin Fulani Hunturbe. Ance Sarkin Kano Dabo ya bi ta garuruwan dake gabashin Kasar Kano tare da jaddada matsayin na Sarkin Kano. Sai dai ance tun kafin Sarkin Kano Dabo ya isa zuwa Sankara tuni Sarkin Fulani Hunturbe ya samu labari. Don haka ne ya shirya mayakan domin fuskantar Sarkin Kano Dabo. Da zuwan Sarki Dabo sai yaki ya rinchabe tsakanin mayakan. An fafata har mayakan Sarkin Kano suka ci karfin yan tawayen Sankara. Daga karshe Sarkin Fulanin Sankara tare da mayakan sa suka gudu. Shi kuma Sarkin Kano Dabo ya shiga cin Sankara tare da jaddada ikon sa a matsayin Sarkin Kano. Daga nan ne Sarki Dabo jiya tare da tunkarar Rano wadda ita ma tayi tawaye.

YAKIN RANO

Mutanen Rano ma sun ki yin mubayi’a ga Sarkin Kano Ibrahim Dabo lokacin da ya zama Sarkin Kano. Don haka ne Sarki Dabo da ya murkushe tawayen mutanen Sankara sai tunkaro Rano.

Ance lokacin da Sarkin Kano Dabo ya isa Rano, sai Barwan Rano ya fito tare da mayaka domin fafatawa da mayakan Sarkin Kano. An buga yaki a daidai tafkin Rano tun safe har la’asar sannan mayakan Sarkin Kano suka ci karumin mayakan Rano tare da kashe Barwan Rano. Sarkin Kano Dabo bai tsaya ba har sai da ya kutsa cikin garin Rano tare da tabbatar da ikon sa a matsayin Sarkin Kano, sannan kuma ya nada Isau a matsayin sabon Sarki ko Hakimin Rano.

YAKIN KUNCI

Bayan Sarkin Kano Dabo ya murkushe tawayen Rano, sai nufi Kunci inda ya samu labarin cewa Dambo babban da ga Dantunku ya yi sansani. Sai dai daga baya Sarkin Kano Dabo ya dawo cikin birnin Kano tare da nada Sarkin Yakin Kano Aliyu domin ya fatattaki Dambo.

Da asuba mayakan Sarkin Kano Dabo karkashin jagorancin Sarkin Yakin Kano Aliyu suka kutsa cikin garin Kunci domin su fatattaki mayakan Dambo dan Dantunku. Sarkin Yaki da mayakan sa sun kewaye garin Kunci tare da bankawa garin wuta. Aka yi kaca-kaca da garin Kunci tare da karkashe mayakan Dambo. Shi kuma Dambo tare da tsirarun mayakan sa sai suka sulale suka gudu.

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button