HausaTarihin Kano

KABILUN FULANI A KANO

Taswira me nuna mazaunan Fulani a Kano. Source : d-maps.com

Kabilun Fulani a Kano ko Kasar Kasar Kano sun kasance wasu rukunan Fulani wanda suka hadu suka samar da gundarin Fulanin Kano. A kalla, Kabilun Fulani a Kano sun kai kusan rukuni fiye da goma.

A bisa tarihi, Kabilun Fulani a Kano sun bayar da gudunmawa wajen kafa Masarautar Kano musamman a lokacin kaddamar da Jihadin Shehu Usman Dan Fodio. Haka kuma sun bayar da gudunmawa wajen ci gaban Kano ta fannin tattalin arziki (economy), ilmin addinin Musulunci (Islamic Education), da kamu kafuwar tsarina mulki mai Kyau (well-organized political institution).

Wasu daga cikin Kabilun Fulani a Kasar Kano sun kasance yanzu yankunan su suna karkashin Masarautar Dutse ko Ringim. Domin kuwa muna so me karatu ya gane cewa Masarautun Dutse da Ringim sun kasance a da karkashin Masarauta ko Kasar Kano a matsayin gundumomin hakimai. Kirkiro Jihar Jigawa ne kawai ya sa yankunan suka bar ikon Sarkin Kano.

Asalin Fulani

Tarihin salin Fulani ya kasance wani abu wanda har yanzu ba’a samu hakikanin gaskiyar labari ba. Sai dai masana tarihi daban-daban sun samar da bayanai akan asalin Fulani.

Tarihi mafi shahara akan asalin Fulani shine wanda ya bayyana cewa Fulani a matsayin su na makiyaya dabbobi masu yawo daga guri zuwa guri sun samo asali ne daga Gabas wato wajejen kasar Jordan a yanzu. Tarihin ya kara da cewa Fulanin sun tsallako Kogin Nilu (Nile River) ta cikin kasar Misra (Egypt) tare da watsuwa cikin yankunan Africa ta Arewa (North Africa) irin su Libya, Algeria, Morocco. Daga bisani kuma suka gangaro zuwa kasashen Yammacin Africa musamman Senegal, Guinea, da kuma Mali. Sai dai kuma tarihin ya nuna cewa yaran Fulatanci ya samu tare da bunkasa a yankin da Fulani suka fara yin kaka-gida wato Yankin Sene-Gambia dake tsakanin Senegal da Gambia.

Shigowar Fulani Kasar Kano

Fulani sun shigo Kasar Kano ko Kasar Hausa ne bayan da suka kwararo daga masaukin su na farko dake yankunan Futa Toro da Futa Djallon.

Sai dai tarihi ya nuna cewa sanannun kungiyoyin Fulani sun fara shigowa ne a wajejen karni na sha hudu wato a turance 14th century. A wannan lokaci wasu kabilun Fulani da ake kira da Wangarawa karkashin Abdurrahman Zaite daga kasar Mali sun shigo Kasar Hausa musamman Kano da Katsina domin yada addinin Musulunci. Saboda haka tun daga wannan lokaci aka yi ta samun shigowar Kabilun Fulani a Kano.

Rabe-Raben Kabilun Fulani a Kasar Kano

Kamar yadda aka fara fada a baya, Kasar Kano tana daya daga cikin manyan Kasashen Hausa wanda kungiyoyin Fulani suka zo suka zauna tun misalin karni na sha hudu. Wasu daga cikin Fulanin sun zo ne domin yin Wa’azin addinin Musulunci da koyarwa, wasu kuma sun shigo ne domin yin kiwo a gefen gulabe da fadamu. Wasu daga cikin masana tarihin Kasar Kano sun bayyana kungiyoyin Fulani da suka shigo suka yi kaka-gida a Kasar ta Kano sun kai kimanin ashirin. Don haka ne zasu kawo muku lissafin Kabilun Fulani a Kano kamar haka :

KABILAR FULANI SULLUBAWA

Kabilar Fulani Sullubawa tana daya daga manyan Kabilun Fulani a Kano musamman saboda yadda suka bada gudunmawa wajen kaddamar da Jihadi a Kasar Kano. Yawancin Fulanin wannan Kabila suna zaune ne a cikin birnin Kano da kuma kewaye. Kabilar Fulani sun kasance mafi shahara da kuma daukaka a tsakanin Kabilun Fulani a Kano musamman kasancewar su wanda mulkin Kasar Kano ko Masarautar Kano yake hannun su. Domin kuwa daya daga cikin shugabannin wannan Kabilar Fulani ta Sullubawa wato Ibrahim Dabo ya mulki Kasar Kano a matsayin Sarki kuma har yanzu jikokin sa ne ke yin mulkin Masarautar Kano.

KABILAR FULANI MUNDUBAWA

Kabilar Fulani Mundubawa na daya daga cikin manyan Kabilun Fulani a Kano musamman saboda yadda suka bada gudunmawa wajen kaddamar da Jihadi a Kasar Kano. Kuma su ma sun kasance suna zaune ne a cikin birnin Kano da kewaye. Haka kuma wannan Kabilar Fulani sun kasance malamai kuma yan kasuwa. Sarkin Kano Malam Sulaimanu ya fito ne daga cikin wannan Kabila.

KABILAR FULANI YOLAWA

Kabilar Fulani Yolawa sun kasance daya daga cikin manyan Kabilun Fulani a Kano musamman saboda yadda suka bada gudunmawa wajen kaddamar da Jihadi a Kasar Kano. Haka kuma sun kasance mafiya tsari a tsakanin Kabilun Fulani a Kano. Fulanin wannan Kabila sun kasance wasu suna zaune ne a yankunan da suka hada da Bichi, Dawakin Tofa da kuma cikin birnin Kano.

KABILAR FULANI JOBAWA

Kabilar Fulani Jobawa sun kasance daya daga cikin manyan Kabilun Fulani a Kano musamman saboda yadda suka bada gudunmawa wajen kaddamar da Jihadi a Kasar Kano. Fulanin wannan Kabila ta Yolawa sun kasance Malamai kuma yawancin mazaunan su suna tsakanin yankunan Wudil, Dawakin Kudu, da Garko.

KABILAR FULANI DAMBAZAWA

Kabilar Fulani Dambazawa ita ma ta kasance daya daga cikin manyan Kabilun Fulani a Kano musamman su ma saboda yadda suka bada gudunmawa wajen kaddamar da Jihadi a Kasar Kano. Kabilar Fulani Dambazawa sun kasance suna zaune ne a yankunan da suke daga Ungogo zuwa Dambatta. Haka kuma wasu suna zaune ne a cikin birnin Kano.

KABILAR FULANI DANEJAWA

Kabilar Fulani Danejawa sun kasance suma babbar Kabilar Fulani a Kano wadda suka bada gudunmawa wajen kaddamar da Jihadi a Kano. Fulanin Kabilar Danejawa suna zaune ne a Yammacin birnin Kano kuma shugaban Kungiyar ya kasance Malam Danzabuwa wanda ya shugabanci kaddamar da Jihadi a Kano.

KABILAR FULANI YARIMAWA

Kabilar Fulani Yarimawa sun kasance daya daga cikin Kabilun Fulani a Kano. Fulani Yarimawa suna da mazaunai ne a gabas da birnin Kano wato yankunan garuruwan Minjibir, Garun-Danga a Kasar Kano yanzu da kuma Babura, Garki, Sankara, da kuma Dabi wanda suke a cikin Jihar a yanzu amma kuma a da suna karkashin Kasar Kano. Su Kabilar Fulani Yarimawa masu alfahari a cikin Kabilun Fulani a Kano. Haka kuma Fulani Yarimawa sun kasance marasa tsoro tare da juriya. Wannan dalilai ne yasa bayan rasuwar Sarkin Kano Sulaimanu Shugaban su Malam Usman Dantunku ya jagorance su suka yi wa Masarautar Kano tawaye tare da kokarin kafa sabuwar Masarauta a yankin arewacin Kano. Sai dai kuma bayan an kwashe shekaru kimanin bakwai ana gwabza yaki tsakanin su da mayakan Masarautar Kano, ALLAH YA bawa Sarkin Kano Ibrahim Dabo nasarar fatattakar shugaban su wato Dantunku wanda ya gudu zuwa arewa tare da kafa Masarautar Kazaure. Don haka ne iyalan Gidan Sarautar Kazaure tare da yawancin Fulanin yankin suka kasance Kabilar Fulani Yarimawa.

KABILAR FULANI GYANAWA

Kabilar Fulani Gyanawa sun kasance daya daga cikin Kabilun Fulani a Kano. Fulanin wannan Kabila sun kasance malamai masu koyo da koyar da addinin Musulunci. Gyanawa suna zaune ne a Yankunan Da suka fara daga Dawakin Kudu zuwa Gaya,wasu kuma daga cikin su suna zaune a cikin birnin Kano.

KABILAR FULANI YALLIGAWA DA JALLIGAWA

Wadannan Kabilun Fulani na Yalligawa da Jalligawa sun kasance suna zaune a yankunan suka fara daga Dutse zuwa Birnin Kudu wanda a yanzu suke karkashin Kasar Dutse wadda a da duk suna karkashin ikon Masarauta ko Kasar Kano ne. Kabilun Fulani Yalligawa da Jalligawa sun kasance masu alfahari da juna a matsayin abu daya wanda hakan ne yasa ake kiran su a dunkule da sunan “Barnawa”

Ahmad Abdullahi, BA History

My name is Ahmad Abdullahi, I was born on 10th March, 1994 in Garun-Danga Town, Gabasawa L.G., Kano State. I attended FCE Demonstration Primary School from 2002 to 2007, FCE Staff Secondary School from 2007 to 2013, and Northwest University, Kano from 2013 to 2017, where I obtained bachelor degree in History.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published.

Back to top button